✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake sauraron karar Atiku kan nasarar Tinubu a zaben 2023

An dage sauraron karar da Jam'iyyar APM ta shigar zuwa ranar 16 ga watan Mayu da muke ciki

Kotu za ta fara sauraron karar da jam’iyyar PDP da dan takarar na shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, suka shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na Jam’iyyar APC a zaben.

A yayin zaman na ranar Talata, alkalin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa na 2023, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya dage sauraron karar da Jam’iyyar APM ta shigar na kalubalantar nasarar Tibubu, zuwa ranar 11 ga watan Mayu da muke ciki.

Tuni lauyoyi da sauran ma’ikata da wakilan jam’iyyu da ’yan jarida da ma ’yan kallo suka kasa, suka tsare a cikin kotun domin ganin yadda shari’ar za a kaya.

A ranar Litinin kotun ta fara zama a kan kararraki biyar da aka shigar gabanta kan zaben, inda Mai Shari’a Tsammani ya ba da tabbacin samun adalci ga daukacin bangarorin da ke shari’ar.

A zaman ranar kotun ta yi watsi da karar Jam’iyyar AA, wadda ta sanar cewa ta jane karar da ta shigar, lamarin da ta rage adadin kararrakin kalubalantar zaben Tinubu  zuwa hudu.

Alkalin da ke jagorantar kotun ya sanya Talata a matsayin ranar sauraron kararrakin da PDP da Atiku da kuma Jam’iyyar APM — kafin dage karar APC zuwa ranar Alhamis.

A ranar Laraba kuma za ta saurari karar da Jam’iyyar LP da takararta na shugaban kasa, Peter Obi gami da Jam’iyyar APP.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai a sanar cewa Tinubu na APC ya lashe zaben da kuri’u 8,794,726.

Wanda ya zo na biyu shi ne Atiku Abubakar na PDP da kuri’u 6,984,520 a yayin da Peter Obi na LP ya zo na uku da yawan kuri’u 6,101,533.

Sai dai duk da haka, Atiku da Obi sun garzya gaban kotun suna neman ta soke zaben Tinubu wanda tuni INEC ta ba shi takardar shaidar zama zababben shugaban kasa.

Shugaban kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani ya ba wa bangarorin da ke shari’ar tabbacin samun adalci.

A halin yanzu dai kasa mako uku ya rage a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16.