✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace shugaban karamar hukuma a Taraba

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba, Boyi Manja, bayan sun kashe dan sanda mai ba shi kariya.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba, Boyi Manja, bayan sun kashe dan sanda mai ba shi kariya.

Aminiya ta gano cewa ’yan ta’addan sun sace shugaban karamar hukumar ne a lokacin da suke tafiya a cikin motarsa ta ofis a yankin Kofar Amadu da ke kan hanyar Takum zuwa Wukari a ranar Lahadi.

Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yankin Kofar Amadu dai ya yi kaurin suna da ayyukan ’yan bindiga inda suka sha kashe matafiya tare da yin garkuwa da wasu.

Yawan ayyukan ’yan bindiga a kan hanyar ta kai ga sai da aka girke rundunar tsaro ta hadin gwiwa domin kare matafiya.

Aminiya ta gano cewa duk da haka, a ’yan makonnin da suka gabata ayyukan ’yan bindiga sun ci ga a kan hanyar.