Kotu ta fara sauraron shaidu a shari’ar kisan gilla da aka yi wa Manjo-Janar Mohammed Idris Alkalina Jihar Filato.
Babbar kotun jihar ta fara zamanta da misalin karfe 9 ma safiyar Laraba inda mutum 21 da ake zargi da kisan Janar Idris Alkali da kuma wakilan Rundunar Sojin Najeriya suka hallara a zauren Babbar Kotun jihar mai lamba biyu.
Kotun za ta yi zaman ne shekara biyarbayan kisan gilla da ’yan bindiga suka yi wa Janar Idris Alkali watan Satumban 2018 a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.
A watan Nuwamban 2018 Rundunar Sojin Najeriya ta gano gawarsa Manjo-Janar a cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet a Gundumar Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato.
Rundunar Sojin ta bayyana cewa a cikin wadanda aka kama bisa zargin bacewar marigayi Janar Alkali ne ya sanar da jami’anta cewa an jefa gawarsa a rijiyar da ta gano marigayin.
Rundunar sojin ta bayyana cewa samun bayanin ne ya sanya ta fara aikin janye ruwan rijiyar a safiyar shekaranjiya Laraba, kuma ba tare da bata lokaci ba ta gano gawar marigayin. Bayan an ciro gawar daga cikin rijiyar ne aka lullube ta a cikin wata jakar leda mai launin tutar Najeriya, kore da fari.
Janar Mohammed ya ce mutum shida daga cikin takwas da ake zargi da hannu wajen bacewar Janar Alkali suna tsare a hannun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Filato.
Idan ba a manta ba dai Janar Alkali ya bace ne a ranar 3 ga Satumba, 2018 a kan hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi, inda bayanin sirri ya tabbatar da bacewarsa a yankin Dura Du da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, kusa da kauyen tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata, Dabid Jonah Jang.
Rundanar Sojin ta yi amfani da na’urar bincike mai suna tracker inda ta gano har kududdufin da aka jefa motar Manjo Alkali a ranar 29 ga Satumba, 2018. A ranar Juma’ar makon jiya ma Rundunar Soji ta gano wani karamin kabari da aka yi zargin an binne Janar Alkali bayan an kashe shi, inda kuma aka sake tone gawar tasa, a yanzu kuma aka gano gawarsa a rijiya shekaranjiya Laraba.
Janar Mohammed ya ce rundunarsu ba za ta huta ba har sai ta tabbatar da an hukunta duk wadanda suke da hannu a bacewar Janar Alkali.