✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyyar Malam Adamu Fika (1933-2023)

Wazirin Fika, tsohon Shugaban Ma'aikatan Najeriya, kuma tsohon Kwamisihinan Kudi na Jihar Arewa maso Gabas, Malam Adamu Fika ya rasu yana da shekaru 90 a…

Fadar Sarkin Fika ta ayyana karfe 4 a matsayin lokacin jana’izar Wazirin Fika, Malam Adamu Fika, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

Sakataren Masarautar Fika, Ali Gimba Fika ya sanar da cewa a yau Laraba za a yi jana’izar a Babban Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello (Sultan Bello) da ke garin Kaduna.

Iyalan Adamu Fika sun bayyana cewa ya rasu ne a hanyarsa ta dawowa Najeriya daga Birtaniya, inda ya yi jinya.

Hassan Gimba Ahmed, wani makusancin iyalan Alhaji Adamu Fika, ya ce “Allah Ya dauki ransa ne cikin jirgi a sararin samaniya a hanyar dawowa Najeriya daga Birtaniya; Allah Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.”

Martabar Malam Adamu Fika

Marigayi Wazirin Fika, Alhaji Adamu Fika, wanda aka haifa a shekarar 1933 dattijo ne da ake girmamawa a Najeriya kuma gogaggen jami’in gwamnati ne.

A lokacin rayuwarsa ya rike mukamai da dama ciki har da Shugaban Majalisasr Koli ta Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) da Kwamishinan Kudi na Jihar Arewa maso Gabas, da kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF).

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ne kuma ya rike mukamnin babban sakatare a ma’aikatu daban-daban.

Gwamnatin Tarayya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta CFR a 1992, shekarar da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ta ba shi Digirin Girmama a fannin Shari’a (LL.D Honoris Causa).

Wane ne Adamu Fika?

Shi ne Shugaban Ma’aikatan Najeriya na farko da ya yi murabus saboda bai ji dadin yadda wasu al’amura ke gudana ba a lokacin  da ya ke jagorancin ma’aikata, inda ya fahimci an gurbata ma’aikatan gwamnati

Ilimin Adamu Fika

An haifi Adamu Fika a shekarar 1933 inda ya yi makarantar firamare ta Fika daga 1941-45 da  Borno Middle School, Maiduguri a 1947.

Ya halarci Kwalejin Gwamnati a Kaduna (Kwalejin Barewa da ke Zariya a yanzu) daga 1948-51.

Daga nan ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya 1952-1953 a lokacin tana matsayin Kwalejin Adabi da Kimiyya da Kere-kere ta Najeriya, a matsayin daya daga cikin dalibanta na farko.

Cibiyar Kididdiga da ke London a kasar Birtaniya a 1958 sai Cibiyar Nazarin Cigaba da ke Jami’ar Sussex, da ke Ingila, 1969; sannan Royal Institute of Public Administration, Jami’ar Manchester, UK, 1978.

Mukaman Adamu Fika

Ya kasance Sufeton Ilimi na Lardin Zariya a 1960 sannan aka nada shi na Lardin Adamawa a 1962, sannan a 1962 aka nada shi Shugaban Kwalejin Horaswa ta Tarayyya (FTC) da ke Kaduna.

An nada nada Adamu Fika Mataimakin Sakataren Hukumar Kula da Ayyukan Jama’a na Wucin Gadi 1968–1970, kafin daga bisani a daga likafarsa zuwa Sakataren hukumar a 1970.

Shi ne Kwamishinan Kudi na Jihar Arewa ta Gabas a 1972 inda bayan ya yi aiki na shekaru uku aka mayar da shi  ma’aikacin Gwamnatin Tarayya, inda ya kasance Babban Sakaate a ma’aikatun Harkokin Cikin Gida a 1975.

An nada Adamu Babban Sakatare a Ma’aikatar Kasuwanci ta Tarayya a 1979, dana nan aka nada shi Babban Sakataren Sashen Aikin Gwamnati a Ofishin Shugaban Ma’aikata 1981–1982.

Adamu Fika ya kasance Babban Sakatare a Ma’aikatar Sadarwa 1982-1984; Ma’aikatar ’yan sanda, Ofishin Zartarwa na Shugaban Kasa; Babban Sakatare, Babban Birnin Tarayya kuma Shugaban Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya, Abuja, a 1984.

An nada Malam Adamu Fika Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a 1986, mukamin da ya yi ritaya a kansa a shekarar 1988.

Bayan nan kuma an ci gaba da neman gudummaawarsa a lokuta daban-daban daga gwamnati da sauran bangarori.