Fadar Sarkin Fika ta ayyana karfe 4 na yamma matsayin lokacin jana’izar Wazirin Fika, Malam Adamu Fika, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.
Sakataren Masarautar Fika, Ali Gimba Fika ya sanar da cewa a yau Laraba za a yi jana’izar a Babban Masallacin Sarkin Musulmi Muhammad Bello (Sultan Bello) da ke garin Kaduna.
- Ta’aziyyar Malam Adamu Fika (1933-2023)
- An gurfanar da dan siyasar Kano a kotu kan barazanar dukan malamin addini
Malam Adamu Fika Wazirin Fika shahararre ne kuma gogaggen malami kuma sanannen mai gudanarwa dan asalin garin Fika da ke jihar Yobe an haifeshi a shekarar 1933 a garin Fika dake jihar Yobe.
Adamu Fika shi ne Shugaban Ma’aikatan Najeriya na farko da ya yi murabus saboda bai ji dadin yadda wasu al’amura ke gudana ba a lokacin da ya ke jagorancin ma’aikata, inda ya fahimci an gurbata ma’aikatan gwamnati.
An haifi Adamu Fika a shekarar 1933 inda ya yi makarantar firamare ta Fika daga 1941-45 da Borno Middle School, Maiduguri a 1947.
Ya halarci Kwalejin Gwamnati a Kaduna (Kwalejin Barewa da ke Zariya a yanzu) daga 1948-51.
Daga nan ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya 1952-1953 a lokacin tana matsayin Kwalejin Adabi da Kimiyya da Kere-kere ta Najeriya, a matsayin daya daga cikin dalibanta na farko.
Cibiyar Kididdiga da ke London a kasar Birtaniya a 1958 sai Cibiyar Nazarin Cigaba da ke Jami’ar Sussex, da ke Ingila, 1969; sannan Royal Institute of Public Administration, Jami’ar Manchester, UK, 1978.
Jerin Ayyuka da makaman da Adamu Fika ya yi
Malamin Lissafi da kimiyya a Kwalejin Barewa da ke Zariya – 1956.
Malami a Makarantar Sakandaren Gwamnati, Katsina-Ala, Jihar Benue – 1958.
Sufeton Ilimi na Lardi, Jami’in Ilimi na Lardi, Zariya – 1960.
Sufeton Ilimi, Lardin Adamawa, Yola – 1962.
Shugaban Kwalejin Horaswa ta Tarayya (FTC), Kaduna – 1962;
Mataimakin Sakatare, Hukumar Kula da Ayyukan Jama’a na Wucin Gadi, 1968-1970.
Kwamishinan Kudi, Jihar Arewa maso Gabas – 1972.
Babban Sakatare, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida – 1975.
Babban Sakatare, Kwamitin Kasuwanci na Tarayya – 1979;
Babban Sakatare, Sashen Ayyukan Jama’a, Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya – 1981 – 1982.
Babban Sakatare, Sashen Harkokin ’Yan Sanda, Ofishin Zartarwa na Shugaban Kasa.
Babban Sakatare, Ma’aikatar Sadarwa, 1982-1984.
Babban Sakatare, Babban Birnin Tarayya kuma Shugaban Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya, Abuja, 1984.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, 1986.
Ya yi ritaya daga ma’aikatan gwamnatin tarayya, 1988;
Shugaban Hukumar Kwalejojin Ilimi ta Kasa, 1989-1990.
Sakataren Gudanarwa na Kasa da Gwamnatin Tarayya ta na nada na Jam’iyyar SDP, 1990.
Shugaban Hukumar Gudanarwa na Bankin UBA 1990-1993.
Magatakarda kuma Darakta-Janar na Majalisar Tarayya, 1992-1993.
Shugaban Farko, Hukumar Albashi ta Kasa 1992-1993.
Shugaban Farko, Hukumar Raba Dai-dai ta Kasa 1995-2001.
Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) -2018