Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lakurawa ne sun kashe mutane sama da 15 a wani sabon hari a Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato.
Wani mazauni kauyen Kwalajiya ya ce ‘yan bindigar Lakurawa sun zo kauyen a daren Lahadi har zuwa Asuba ta ranar Litinin inda suka kashe wasu mutane, a yayin da suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
“Bayan sun kashe mana mutane sun tafi da dabbobi masu yawa, duk da mutanenmu sun yi kokari amma yawan maharan da makaman da suke dauke da su ya sa suka fi karfinmu.
“Har zuwa yanzu ba mu san adadin wadanda aka kai asibiti ba domin suna da yawa, sai dai wadanda suka rasu 15 muka yi wa Sallah.
“Muna kira ga jami’an tsaro su mayar da hankali wurin korar mana wadannan ‘yan bindigar don mu samu zaman lafiya a jiha baki daya.”
Babban Jami’in Kungiyar Agaji Red Cross a Sakkwato, Alhaji Abubakar Ainu ya ce harin ya matukar tayar da hankalin mutanen yankin saboda an dauki dogon rabon da a samu irin hakan.
Ainu ya ce, “jami’anmu sun ziyarci kauyen Kwalajiya da ke Mazabar Magoho a garin Tangaza domin jajantawa da kuma halartar Sallar Jana’izar mutanen da ‘yan bindigar suka kashe sama da 15.
“Waxanda suka jikkata an kai su Asibitin Kashi na Wamakko da Asibitin Koyarwa ta Jam’ar Usmanu Danfodiyo da na Kwararru a birnin Sakkwo domin karbar magani.”
Ya ce yankin na cikin wuraren da ke fama da matsalar barayin shanu da masu tayar da kayar baya.
“Wannan lamari ba ya da dadi ko kadan, dubi yadda aka mayar da wasu mata zawarawa aka mayar da wasu yara marayu domin biyan wata bukata wadda addini bai yarda da ita ba. Ina kira ga hukuma ta sake salon yakar ‘yan bindiga da take yi,” in ji Ainu.