✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayu

Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne bayan ɓangaren masu ƙara sun yi tambayoyi ga Manjo-Janar U. I. Mohammed…

Kotu ta ɗage shari’ar kisan Manjo-Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu.

Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne bayan ɓangaren masu ƙara sun yi wa Manjo-Janar U. I. Mohammed mai ritaya tambayoyi game da kisan.

Janar Alkali, wanda ya kasance tsohon shugaban gudanarwa a Hedikwatar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ya ɓace ne makwanni kaɗan bayan ya yi ritaya daga aikin soja, a lokacin da yake hanyar tafiya Bauchi daga Abuja. Mamacin ne yake tuƙa kansa a lokacin da yake tafiyar inda ya biya ta Jihar Filato.

A lokacin da ya ba ce a shekarar 2018, Janar Mohammed shi ne Kwamandan Sansanin Runduna ta 3 kuma ya jagoranci aikin neman da ceto jami’in da ya ɓata.

Shi ne ya jagoranci aikin da ya kai ga gano motar Janar Alkali a wani rami mai zurfi a yankin Du, daga baya kuma aka gano gawarsa a wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da ke gundumar Shen a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu kare kai ya yi wa Janar Mohammed tambayoyi tare da neman ƙarin haske kan bayanan da ya bayar a baya da kuma shaidarsa dangane da mutuwar Janar Alkali.

Tambayoyin, wadanda suka dauki kimanin awanni biyu, sun mayar da hankali ne kan bayanan da ya bayar na farko da kuma waɗanda suka biyo baya game da lamarin.

Bayan zaman kotun, Mai Shari’a Arum Ashom ya sallami shaidan kuma ya tsayar da ranar sauraron karar na gaba.

Lauyan masu gabatar da ƙara, Simon Mom, wanda ya wakilci Babban Lauyan Jihar Filato, bai nuna adawa da dage shari’ar ba.

Daga bisani, alƙali ya dage shari’ar zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu domin masu kare kai su fara gabatar da nasu bayanan kare kansu.