Wata yarinya mai shekara uku kacal a duniya daga cikin daliban Makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke garin Tegina da aka sace ta rasu a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Wata majiya ta bayyana cewar an bar gawar yarinyar yashe a kan hanya dab da hanyar shiga garin.
- Hanyoyin da za a bi don magance matsalar tsaro — Janar Kukasheka
- Tsuntsun da ke zama kamar lema don farautar kifi
Bincike ya gano cewar yarinyar ta rasu ne sakamakon zazzabi da kuma farbaga a dalilin harbe-harbe da ’yan bindigar ke yi.
Daya daga cikin mahaifan yaran da aka sace, Tanko Zegi ya tabbatar da rasuwar yarinyar ga manema labarai.
Zegi ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnati ta yi burus da halin matsalar tsaro da jihar ke fuskanta tun bayan sace daliban.
Kazalika, ya shaida cewar babu wani jami’in gwamnati da ya ziyarci garin don jajanta musu game da satar yaran nasu.
Kazalika, iyayen daliban sun jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar kan yadda yake tashi fadi don ganin yaran sun kubuta cikin koshin lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa, tuni dai daga cikin iyayen daliban da aka sace suka riga mu gidan gaskiya sakamakon damuwa da suka shiga tun bayan sace ’ya’yansu da ’yan bindigar suka yi.
Ana iya tuna cewa, a karshen watan Mayun da ya gabata ne ’yan bindiga suka auka wa makarantar ta Salihu Tanko Islamiyya da ke garin Tegina inda suka yi awon gaba da gomman dalibai kananan yara da yawansu ya haura 130.