✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yar Shekara 14 Ta Mutu A Dakin Otal  

Rundunar na ci gaba da bincike domin gano musababbin mutuwar yarinyar.

Wata ‘yar shekara 14 mai suna Shallon Ebitare, ta mutu a yayin da ta ke tsaka da sharholiya da masoyinta mai shekara 17 a wani dakin otel da ke Yenagoa a Jihar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, yayin da yarinyar da suka kebe da saurayinta mai suna Lucky Okubo, a wani dakin otal da ke Yenagoa da niyyar biyan buƙatar juna. 

Rahotanni sun bayyana cewa yarinyar ta mutu ne sanadiyyar faduwa a bandaki. 

Faruwar hakan ke da wuya aka garzaya da ita zuwa Asibitin Tarayya (FMC) da ke Yenagoa, domin duba, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarta. 

An bayyana cewa kananan yaran biyu sun fara soyayya ne ‘yan watanni kafin faruwar lamarin. 

Tuni dai jami’an rundunar ‘yan sandan jihar, suka kama saurayin bisa zargin kisan kai domin ci gaba da bincike. 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Musa Muhammed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

“Bayan gudanar da binciken sirri, an kama wanda ake zargi da kashe Shallon Ebitare, ‘yar shekara 14.

“Bincikenmu ya bayyana mana cewa yaron mazaunin unguwar Akaibiri a Karamar Hukumar Yenagoane.”

Kawo yanzu dai, rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wanda ake zargin. 

Matashin ya ce shi ya dauki yarinyar zuwa wani otal, domin biyan buƙatar juna. 

“Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa marigayiyar ta je bandaki ne domin yin wanka, amma sai ta fadi, inda ta samu raunuka.

“Daga baya ya gayyaci manajan dtal ɗin wanda ya taimaka wajen kai marigayiyar zuwa FMC, Yenagoa, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

Wanda ake zargin yana tsare a sashen SCID, Yenagoa yayin da ake ci gaba da bincike da nufin gano musabbabin mutuwar yarinyar.