Wata sojar Amurka ’yar asalin Najeriya, Amanda Azubike, ta sami karin girma zuwa mukamin Birgediya-Janar a Rundunar Sojan Amurka.
Babban Kwamnandan Rundunar Sojin Kasa ta kasar, Manjo-Janar Antonio V. Munera, ne ya sanar da karin girman a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.
- PDP ta kori tsohon dan takararta na Gwamna a Ogun daga jam’iyyar
- Gwamnati ba ta sayen makamai a wajenmu – Kamfanin sarrafa makamai na Najeriya
“Muna taya murna ga sabuwar jami’ar da ta sami karin girma a Rundunar Sojan Kasa ta Amurka, Birgediya-Janar Amanda Azubike! A yau, ta sami karin girmanta daga Janar James Rainey, a yayin wani taro da ya sami halartar iyalai, abokai da sauran shugabannin al’umma,” kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na Twitter.
An dai haifi Amanda ne a birnin Landan na Birtaniya, kuma iyayenta asalinsu ’yan Najeriya ne.
Ta fara aiki a matsayin sojar Amurka ne a shekarar 1994, sannan ta zama matukiyar jirgin saman rundunar, bayan ta kammala karatu a Makarantar da Horar da Direbobin Jirgin Sama ta Amurka.
Ta ci gaba da aiki a rundunar a matsayin jami’ar hulda da jama, bayan ta shafe shekara 11 a fagen tukin jirgin saman.
Yanzu haka, ita ce Mataimakiyar Kwamanda a Rundunar Sojin Kasa ta Amurkar, kuma a baya ta taba zama babbar jami’ar soja mai mai bayar da shawara a Ofishin Sakataren Tsaron Amurka.