✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yar kwallon Falcons ta yafe wa NFF Naira miliyan 1 da dubu 200

’Yar kwallon kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da ake wa lakabi da Super Falcons mai suna Courtney Dike ta yafe wa Hukumar NFF…

’Yar kwallon kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya da ake wa lakabi da Super Falcons mai suna Courtney Dike ta yafe wa Hukumar NFF alawus dinta na Naira miliyan 1 da dubu 200 kwatankwacin Dala dubu 7 a matsayin kudin alawus din da aka ba kowace ’yar kwallon da ta halarci gasar cin kofin dunina na mata (U-20 FIFA Women’s Competition) da ya gudana a Kanada, inda Najeriya ta kasance ta biyu.

’Yar kwallon kanwa ce ga dan kwallon Super Eagles Bright Dike, ta ce ta yi wa Najeriya wasa ne don kishi ba don kudin da za a ba ta ba don haka ta yanke shawarar kin amsar alawus din nata.
Dokta Sanusi Mohammed, shugaban sashen shirya wasanni a Hukumar NFF ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce ya yi mamaki a lokacin da iyalan Dike suka ki karbar alawus din Courtney a lokacin da suka ziyarci gidan don mika musu hakkin ’yarsu.
Ita dai Courtney tana zaune ne a Amurka, mahaifiyarta ta ce ba su karbi kudin ba ne don ya yi wa ’yarsu yawa. “”Ba ta dama ta yi wa Najeriya wasa kadai ya isa ba lallai sai an biya ta makudan kudi irin wannan ba”, inji mahaifiyar Dike.
Wannan hali ya sa ya yi hannun riga da sauran ’yan wasan da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa. Idan za a tuna a gasar cin kofin duniya da ya gudana a Brazil, ana gab da yin wasa a tsakanin Najeriya Super Eagles da Faransa ne, ’yan kwallon Najeriya suka kekasa kasa suka ce sai an biya su alawus dinsu kafin su buga wasan al’amarin da ta sa duk da biyansu da aka yi sun samun rashin nasara a wasan.