Mataimakiyar mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Falcons Tochukwu Oluehi ta samu nasarar samun kulob a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don cigaba da buga kwallo a kulob din Al-Wahda da ke Abu Dhabi.
Jami’in hulda da ’yan jaridu na kungiyar Falcons Gracious Akujobi ce ta sanar da haka ga ’yan jaridu masu farautar labarin wasanni a ranar Litinin da ta wuce a Abuja.
Akujobi wacce ta ki bayyana adadin kudin kwangilar ta ce ’yar kwallon tuni ta bar kasar nan zuwa Abu Dhabi don cigaba da wasa.
Ta ce duk da yake ’yar kwallon ta canza sheka zuwa Abu Dhabi hakan ba zai hana ta dawowa gida don buga wa kasar nan wasa idan an gayyace ta ba.
’Yar kwallon Falcons ta samu kulob a Hadaddiyar Daular Larabawa
Mataimakiyar mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Falcons Tochukwu Oluehi ta samu nasarar samun kulob a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) don…
