✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tabbatar da zaben Gwamna Mutfwang na Filato

Kotun ta kori karar da Jam'iyyar APC ta shigar na kalubalantar nasarar Gwamna Mutfwang a zaben da aka gudanar ranar 18 ga Maris, 2023.

Kotun korafin zaben ta tabbatar da nasarar Gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP a zaben Gwamann Jihar Filato.

Kotun ta kuma kori karar da dan takarar Jam’iyyar APC Nentawe Yilwatda ya shigar na kalubalantar nasarar Gwamna Mutfwang a zaben.

Yilwatda ya je kotun ne yana neman ta umarci Hukumar Zabe ta Kase (INEC) karbi kuri’un da ya samu a wasu rumufan zaben 14 da hukumar ta soke, ta kuma ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Ya dauki matakin zuwa kotun ne bayan INEC ta sanar da Mutfwang a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Da yake yanki hukunci, shugaban kotun sauraron karar, Mai Shari’a R. Irele- ifineh ya bayyana cewa batun da Yilwatda ya shigar kan tsarin jam’iyyar PDP abu ne na kafin zabe, kuma ba shi da hurumin kalubalantar su.

Ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta sake gudanar da babban taronta na jihar ranar 25 ga watan Satumba, 2021 bisa umarnin Mai Shari’a S.P. Gang na Babbar Kotun Jos.

%d bloggers like this: