Wasu da ake zargin ’yan sa-kai ne a sun kashe sojoji uku da ’yan banga biyu a yankin Umaisha da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.
Ana zargin ’yan sa-kan sun kai wa jami’an tsaron harin kwanton bauna ne a yankin Umaisha, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar.
Aminiya ta gano cewa wasu mahara sun kai hari a kwanan nan a kauyen Okudu inda suka kakkashe jama’a.
Kasa da mako guda kenan bayan a ranar 1 ga watan Fabrairu wasu mahara sun kashe mutane uku suka kona kadarori na miliyoyin kudi a kauyen.
An girke sojoji a kauyukan Katakpa da Okudu ne domin samar da zaman lafiya, sakamkon rikicin da aka samu tsakanin kauyukan biyu.