Shugabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun shiga wata ganawar sirri tare da Shugaban Kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja.
Rahotanni sun ce ganawar na zuwa ne jim kadan bayan kungiyoyin sun kammala gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai game da halin da aka jefa ’yan kasa sakamakon cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
- Yanzu-yanzu: Tinubu ya aike wa majalisa karin sunayen ministoci
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
Cire tallafin mai da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi tun a jawabinsa na bayan karbar rantsuwar fara aiki ya sa farashin fetur tahin gwauron zabo daga N197 zuwa 620.
Hakan ya haifar ta hauhawar farashin kayan masarufi da na sufuri, wanda kawo yanzu ’yan kasar ba su ga alamar sassautawarsu
Hakazalika, duk da karin farashin da aka samu na wadandannan kayayyakin bukatu na yau da kullum, har yanzu ba a yi musu karin albashi ba.