Manyan hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka suna tattaunawa a Najeriya kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
Wakilinmu da ke halartar taron ya bayyana cewa manyan hafosohi tsaron kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar da Guinea, inda sojoji suka yi juyin mulki sun kaurace wa taron da ke gudana a Hedikwatar Tsaron Najeriya da ke Abuja.
- An kama wanda ya sace wa fasinja N1m a cikin jirgin sama
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
Mahalarta taron wanda shugaban rundunar sojin ECOWAS, Janar Christopher Musa yake jagoranta, su ne manyan hafoshin kasashen Togo, Sierra Leone, Senegal, Nigeria, Ghana, Liberia, Guinea Bissau, Gambia, Cote’Divoire, Cabo Verde a kuma Jamhuriyar Benin.
Taron na zuwa ne mako guda bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar.
Kwana biyu ke nan kuma bayan kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar da Guinea, inda sojoji suka yi juyin mulki, sun yi barazanar yakar dakarun ECOWAS da kasashen Turai da ke neman yi wa sabuwar gwamnatin sojin Nijar katsalandan.
ECOWAS ta umarci masu juyin mulkin Nijar su mika mulki ga Mista Bazoum wanda ke tsare a hannunsu tun ranar Talata, ko kuma ta tura dakaru su murkushe su, amma suka yi biris da umarnin. Hasali ma tun farko sojojin sun bukaci kasashen waje su cire bakinsu a matsalar da suka kira ta cikin gida a Nijar
Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan jinkai a Nijar domin nuna adawa da juyin mulkin; ita ma Faransa babbar kawar gwamnatin Bazoum ta janye tallafin da take ba wa kasar, ta kuma fara kwashe fararen hularta zuwa gida.