✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wanda ya sace wa fasinja N1m a cikin jirgin sama

Ya sace wa wani fasinja kudi a yayin da suke tafiya a sararin samaniya a jirgin kamfanin Air Peace.

Wani mutum ya shiga hannu bayan da ya sace wa wani fasinja Naira miliyan daya a yayin da suke tafiya a jirgin kamfanin Air Peace.

Dubun barawon ta cika ne a hanyar jirgin na zuwa Fatakwal daga Abuja a ranar Laraba 27 ga watan Yuli, 2023, kwanaki kadan bayan an kama fasinjar kamfanin jirgi na Ibom Air ta sace wa wani fasinja kwamfutarsa, laptop.

Kakakin kamfanin Air Peace, Stanley Olisa, ya ce fasinjar ta sace kudin da ke ajiye a cikin wata ambula ne, amma mai kudin ya kama ta dumu-dumu, ya kuma sanar da ma’aikatan jirgin.

Olisa ta ce, barauniyar ta sace kudin ne bayan da, “ta dauki jakar kwamfutar wani fasinja da ke aje a akwakun sama jirgi, ta cire ambulan din da kudin (Naira miliyan daya) ke ciki, sannan ta sanya kwamfutar a wani akwaku na daban, ta je ta zauna a wani kujera da babu kowa a bayan jirgin.

“Yana cikin wadan da suka yi saurin fita daga jirgin sabanin tsarin fita da ma’aikata suka sanar, amma aka kama shi, aka kwace kudin. An kuma same shi da dauke da kudaden kasashen daban-daban”.

An dai mika shi ga jami’an tsaro na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) domin damka shi a hannun ’yan sanda du gudanar da bincike.

’Yan sanda sun sanar cewa an sake shi bayan ba da belin sa, kuma da wuya a gurfanar da shi, saboda mai kudin ya nuna ba ya son hakan.