Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu ya ce ba kowanne aiki da za su yi yayin gudanar da babban zabe mai zuwa ba ne ke bukatar sai an yi amfani da tsabar kudi ba.
Ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, jim kadan bayan ya kammala zagayen duba wurin da ake horar da ma’aikatan wucin gadi na zaben da kuma duba kayayyakin da aka tanada a cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa da ke Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja.
- Dan bindiga ya harbe tsohuwar matarsa da wasu mutum 5
- ISWAP ta sako ma’aikacin lafiyar da ta sace a Borno wata 11 da suka gabata
An dai yi ta nuna damuwa a ’yan kwanakin nan kan cewa akwai yiwuwar wahalar tsabar kudin da ake fuskanta yanzu a Najeriya ta sa a dage zabukan na ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma 11 ga watan Maris mai zuwa, sakamakon sauya fasalin kudin da aka yi.
Hakan dai ya sa Farfesa Yakubu ya jagotanci tawagar hukumar zuwa ga Babban Bankin Najeriya (CBN), inda bankin ya ba su tabbacin samun dukkan tsabar kudin da suke da bukata domin zaben.
To amma da yake jawabi ranar Asabar a Abuja, Farfesa Yakubu ya kore fargabar da ake da ita kan karancin kudaden.
Ya ce, “Mun ziyarci CBN a makon da ya gabata a kan matsalar kudi, a kan wasu ayyukan da za mu yi a ranar zabe.
“Amma galibin abubuwan da za mu yi a ranar, za mu iya tura kudin ta bank, ba ma bukatar tsabar kudi. Wasu abubuwan kuwa masu matukar muhimmanci wadanda dole sai da tsabar kudi su suka sa muka je CBN, amma ba ma su suka fi yawa ba.
“CBN ya ba mu tabbacin cewa babu wata matsala da za a fuskanta, saboda haka babu wani abun damuwa a kai.
Shugaban na INEC ya kuma tsaya kai da fata cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Tarayya ranar Asabar mai zuwa.
Game da batun tsaro kuwa, Shugaban na INEC ya ce zanga-zangar da ake yi a wasu sassan Najeriya a kan karancin kudi abar damuwa ce, inda ya ce za su tattauna hanyoyin magance ta da jami’an tsaro, tare da bayar da tabbacin samar da tsaro a dukkan rumfunan zaben kasar.