Dukkanin yankuna hudu da aka mamaye na Ukraine sun kada kuri’ar zama cikin kasar Rasha bayan zaben raba gardama da aka gudanar, a cewar jami’an jami’an gwamnatin Rasha.
Mafi yawan kasashen duniya dai ba za su amince ba da sakamakon da ke zuwa bayan an ga jami’ai dauke da makamai sun bi gida-gida suna karbar kuri’u.
- DAGA LARABA: Yadda ‘Sakacin Ma’aikata’ Ke Lakume Rayuka A Asibitin Murtala
- Sarkin Saudiyya ya nada dansa a matsayin Fira Minista
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya James Cleverly, na daya daga cikin ‘yan siyasar yammacin duniya da a baya suka bayyana kuri’un da aka kada a yankunan Luhansk da Donetsk da suka ayyana kansu a matsayin jamhuriyya da kuma yankunan Kherson da Zaporizhzhia a matsayin kuri’ar soki-burutsu.
Hakan na zuwa ne bayan da jami’an zabe da Rasha ta tura sun sanar cea kashi 93 cikin 100 na kuri’un da aka kada a yankin Zaporizhzhia na goyon bayan komawarsu karkashin kasar Rasha.
Jima’an su kuma bayyana cewa kashi 87% na kuri’un da aka kada a yankin Kherson na Kudancin Ukraine da kashi 98% na Luhansk da kuma kashi 99% a Donetsk, duk sun amince da su koma Kasar Rasha.
An fara kada kuri’ar raba gardama ne a ranar 23 ga Satumba, ind aka rika ganin jami’ai dauke da makamai suna bi gida-gida suna karbar kuri’u.
Jami’ai masu samun goyon bayan Rasha a yankuna hudu da ta mamaye a kudanci da Gabashin Ukraine sun ce an rufe rumfunan zabe da yammacin Talata bayan kwanaki biyar na kada kuri’a.
Dubban mazauna yankunan dai sun riga sun tsere saboda yakin.
Ana ganin sakamakon da aka sanar da ya kawo wani sabon yanayi mai hatsarin gaske a yakin da Rasha ta kwashe watanni 7 ana yi a Ukraine.
Ana zargin Rasha za ta yi amfani da shi a matsayin hujjar da za ta iya hade yankunan hudu zuwa cikin kasarta.
Hakan na iya faruwa nan da zaran Juma’a.
A halin da ake ciki, Rasha ta tsananta gargadin cewa za ta iya amfani da makaman nukiliya don kare yankinta, gami da sabbin yankunan da aka yi zaben raba gardama.