Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa.
Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas.
- Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas
- Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno
Bisa ga bayanai, Amurka za ta samu wani kaso mai yawa daga ribar da za a samu, wanda zai iya kai wa Dala biliyan 500.
Duk da cewa ba a bayyana batun tallafin tsaro a cikin yarjejeniyar ba, ministar shari’ar Ukraine, Olha Stefanishyna, ta ce akwai wasu muhimman batutuwa da Ukraine za ta amfana da su.
A ranar Juma’a mai zuwa ne shugaba Volodymyr Zelenskyy, zai tafi Amurka don ganawa da shugaba Donald Trump domin kammala yarjejeniyar.
Ukraine za ta riƙa saka kaso 50 na ribar da ta ke samu daga ma’adinanta a wata gidauniya ta haɗin gwiwa da Amurka, kuma wani ɓangare na kuɗin za a yi amfani da shi wajen sake gina ƙasar.