Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin tuntuɓar takwaransa na Rasha Vladimir Putin da zummar tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Trump ya shaida wa manema labarai hakan a cikin jirgin shugaban ƙasa na Airforce One a kan hanyarsa ta zuwa Washington daga Florida cewa yana ƙoƙarin ganin cewa yaƙin ya zo ƙarshe.
Trump ya bayyana cewa an yi aiki sosai a game da kawo ƙarshen wannan rikici a cikin ƙarshen makon da ya gabata.
Trump na ƙoƙarin samun goyon bayan Putin a game da tayin tsagaita wuta na kwanaki 30, wanda Ukraine ta amince da shi a makon jiya.
Kazalika, Trump ya ce za su tattauna batun iyakokin kasa da kuma tashoshin makamashi da dai sauran muhimman batutuwa
Sai dai ana ci gaba da miƙa tayin ne a yayin da dukkannin ɓangarorin ke ci gaba da yi wa juna luguden wuta ta sama, har sai da sojin Rasha suka kusan fatattakar dakarun Ukraine a yankin Kursk.
A ranar Juma’a, Fadar Gwamnatin Rasha, Kremlin ta ce shugaba Putin ya aike da saƙo zuwa ga Trump a game da tsagaita wuta ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, wanda ya ziyarci Moscow, inda yake bayyana aniyar tsagaita wuta amma da taka-tsantsan.