✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya umarci tsagaita wuta a Ukraine albarkacin bikin Ista

Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga tsakani wajen ganin an yi musayar fursunonin cikin nasara tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Vladimir Putin a yau Asabar ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a wanan ranar ta Ista da kuma gobe Lahadi.

Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura.

Haka kuma, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi na sama da mutum 500 — kuma mafi girma tun bayan fara yaƙi a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya ce ƙasarsa ta karɓi sojoji fursunonin yaƙi akalla 277 waɗanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Telegram.

Ita ma ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta karɓi sojojinta 246 daga Kiev, waɗanda a halin yanzu ke ƙasar Belarus wacce ke kawance da Rasha kafin daga bisani a maida su gida.

Kazalika, hukumomin Moscow da Kiev sun jinjina wa UAE wajen gudanar da wannan gagarumin aiki cikin kwanciyar hankali.

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa dai ce ta shiga tsakani wajen ganin an yi musayar fursunonin cikin nasara tsakanin ƙasashen biyu da suka shafe shekaru uku suna gwabza yaƙi.

Bayanai sun ce Rasha ta kuma yi iƙirarin cewa ta kusan ƙwato yankunan da sojojin Ukraine suka mamaye tun lokacin bazarar shekara ta 2024 a yankin Kursk da ke kan iyakar Rasha.

Ƙasashen duniya na ci gaba da kira na ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙi, duk da cewa Rashan da Ukraine kowanensu na iƙirarin samun galaba a yaƙin.