Ga alamu yankin Karamar Hukumar Faskari na neman zaman tarkon mutuwa sakamakon hare-haren ‘yan bindigar da suka zarce irin na Batsari.
Harin farko da ya yi muni a yankin shi ne wanda aka kai a garin ‘Yankara bayan kashe wata mata da ake yi wa lakabi da uwar daba.
A yanzu kuma a cikin kwanakin da ba su wuce hudu ba an kashe mutum sama da 70 a yankin. A garin Kadisau kadai an kashe mutane sama da 60 kamar yadda rahotanni suka nuna.
Kusan babu ranar da ba a kai hari a wannan yankin inda a ranar Juma’a aka kai hare-hare a kauyukan Unguwar Kafa, Unguwar Mai Dawa da kuma ‘Yankara.
- ‘Yan bindiga sun kara kashe basarake a Katsina
- ‘Yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki
- Rashin Tsaro: Matasa sun yi bore a Katsina
Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar yankin kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Honarabul Dalhatu Tafoki ya ce hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutum 8.
Mataimakin Kakakin Majalisar wanda yake shaida haka a cikin alhini da kuma damuwa game da irin yadda yankin ya zama tarkon mutuwa, ya ce babban abin da suka sa gaba yanzu shi ne addu’a tare da kara matsa kaimi ga wadanda hakkin ya rataya a kansu domin daukar matakin da ya dace.
Ko a daren jiya Juma’a 12 ga watan Yuni mahara sun kashe Mai garin Mazoji da ke Karamar Hukumar Matazu, sannan aka dauke dan Magajin Garin Batsari a kan hanyarsa ta zuwa gona.
Ana dai ci gaba da kisan kiyashi, satar shanu, fyade tare da yin garkuwa da mutane a tsakanin yankin da ya faro tun daga Karamar Hukumar Jibiya har zuwa Sabuwa a cikin jihar ta Katsina, duk kuwa da ikirarin da jami’an tsaro ke yi na cewa sun kakkabar da maharan.