Duk yawan hakiman da ke Masarautar Katsina da suka hada da masu zaben Sarki, ’Yandakan Katsina ne kadai ke ba Sarki hannu kai-tsaye don su gaisa, bayan kuma yana daga cikin masu zaben sabon Sarki a masarautar. Alhaji Sada Muhammad Sada shi ne ’Yandakan Katsina Hakimin Dutsinma na yanzu, ya yi wa wakilin Aminiya bayani a kan tarihin wannan sarauta ta ’Yandaka.
Ya ce, “Wannan sarauta ta ’Yandaka ta samo asali ne tun lokacin Habe. Gidan sarautar yana nan a Unguwar ’Yantaba da ke cikin garin Katsina. Kuma a wancan lokaci, masarautar ta ’Yandaka ta fara tun daga wajen Unguwar Yari da ke nan cikin garin Katsina. Daga nan ta shigo ta Sagi, ta tafi har zuwa Kankara wato inda Sarkin Pauwa ke hakimci a yanzu.”
Ya ce an canja wa sarautar suna zuwa Magajin Malam bayan an karbo tuta daga hannun Shehu Ɗan Fodiyo wanda kakanninsu masu rike da wannan sarauta suka yi. Kamar yadda bayanai suka gabata, shi Malam Na-Alhaji na daga cikin mutum uku da suka tafi karbo tuta daga wajen Shehu Dan Fodiyo da nufin su zo su mulki Katsina, wato kowane daya daga cikinsu ya tafi da wannan nufi ne. Shi Malam Na-Alhaji Kakan ’Yandakawan sai Umarun Dunya da kuma Umarun Dallaje.
Dukansu kuma sun karbo wannan tuta inda kowanensu ya biyo hanyarsa daban don shigowa Katsina. Shi Malam Na-Alhaji ya biyo ta Ƙofar ’Yanɗaka,Umarun Dunya ya shigo ta Kofar Sauri yayin da shi Umarun Dallaje ya shigo ta Kofar Kaura kuma shi ne Allah Ya ba sarautar Katsina a wancan lokaci. “Kamar yadda tarihi ya nuna, an ce asalin Sullubawa daga shi Umarun Dunya ne daya daga cikin wadanda suka je karbo tutar. Kuma an ce ya zauna a Unguwar Sullubawa da ke wajen Kofar Guga. To shi Malam Na- Alhaji da ya zo Katsina bayan karbo tutar, daga baya sai ya koma can Sakkwato da zama can kuma Allah Ya karbi abinsa. Dikko dan Malam Na-Alhaji shi ne ya yi sarautar Magajin Malam. A haka abubuwa suka yi ta tafiya. Zuriyar Malam Na-Alhaji ta ci gaba da yin wannan sarauta har zuwa yau,” inji ’Yandakan.
Da Aminiya ta nemi jin ko yaya aka yi wannan sarauta ta baro garin Katsina da kuma canjin suna daga Magajin Malam zuwa sunanta na farko, sai’Yandaka Sada ya ce, “A lokacin ’Yandaka Hassan ne ya zo nan wajen garin Tsauri ya yi gona. To yana tasowa daga can ’Yantaba zuwa gonar duk lokacin damina ya yi noma. To wata rana sai Sarkin Musulmi na wancan lokacin ya taho daga Sakkwato sai hanya ta kawo shi har nan Tsauri. Irin yadda ya ga wurin da dausayi, sai ya nemi jin ko na wane ne. Jin an ce gonar ’Yandaka Hassan ce, sai Sarkin Musulmin ya ce, yana da kyau shi ’Yandaka ya dawo nan da zama. To wannan ne dalilin baro cikin garin Katsina zuwa nan Tsauri. To a nan ne mahaifin Kakana wato ’Yandaka Mani ya ci gaba da mulki har tsufa ya kama shi, domin yana tsoho Turawa suka zo. Sun samu Kakana ’Yandaka Sada na wakilci har zuwa lokacin da mahaifinsa ya rasu. To kuma a wancan lokacin duk mai yin wakilci a garin Kurfi yake zama. To bayan an nada Kakana ’Yandaka Sada, sai Turawa suka ba shi shawarar ya dawo nan Dutsinma da zama domin nan ne tsakiyar inda yake sarauta. Wannan shi ne dalilin maido da gidan Hakimi nan Dutsinma. ’Yandaka Sada ya rasu a a 1940. Sai dai kuma yankin da yake mulki ya ci gaba da raguwa ana sanyawa a wasu yankuna. Kuma tun lokacin da ’Yandaka Sada kakana ya dawo gidan sarautar a nan har yanzu shi ne, wato wannan gidan da muke ciki ni da kai yanzu.
Sannan baya ga wancan tsohon gida da ke Katsina, akwai ma gidan ’Yandaka a cikin garin Batagarawa domin ta zauna karkashinsa. Kazalika, kamar yadda aka sani, Malam Na-Alhaji na daga cikin wadanda suka je neman sarauta a lokacin jihadi, ke nan ya zamo abokin tarayya ta wancan fannin, wannan dalili ne ya sa ’Yandaka ke daga cikin masu zaben Sarki. Sannan shi kadai ne zai iya zama bisa kujera kamar yadda Sarki zai zauna in sun hadu. Sannan zamowarsa aboki a wajen neman sarautar, shi kadai ne ke ba Sarki hannu don su gaisa. Saboda wannan dalili ma ya sa ake yi masa kirari da cewa, ‘Ba Bara ba ne, aboki ne.’
’Yandaka Sada, wanda dan gado ne, ya ce an nada shi wannan sarauta a ranar 16 ga watan Mayu 2009 bayan rasuwar mahaifinsa. Kuma kamar yadda aka sani, duk inda hakimi yake wakilin Sarki ne, sannan kamar yadda muka ambata a baya, yana daga cikin masu zaben Sarki. ’Yandaka ne ke bai wa Sarki Tukunyar Korau a lokacin da ake nada Sarkin. Sannan shi ne ke sanya wa Sarki alkyabba in an yi nadin. Ka ga wadannan duk wasu ayyuka ne na daban.
Hakimin ya bayyana irin ci gaban da masarautarsa ta samu a wannan lokaci da yake bisa wannan kujera ta ’Yandaka. “Wannan masarauta ta hakimi tana da Magaji 16 a karkashinta. Har’ila yau, waccar tuta da aka amso daga Mujaddadi na daga cikin kayan sarauta na alfahari da wannan sarauta ta ’Yandaka ke alfahari da ita. Ai in ka lura, sarauta ce wadda ta jibanci addini daga baya wanda ta haye mana in ka kebe lokacin Habe. Domin shi Malam Na-Alhaji an ce sunan mahaifinsa Malam Usman Ba-Ka-Duba, wanda aka ce asalinsu sun fito daga wajen Tunbuktu ta kasar Mali. A yanzu ni ne ’Yandaka na 16 tun daga kan Dikko ba daga Habe ba. Sannan koda aka nada ni a bisa wannan kujera, da ma nas an jama’ar Dutsinma masu biyayya ne ga masarauta kuma har yanzu suna nan a kan haka. Ga su kuma da hadin kai,” inji shi.