✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yancin kananan hukumomi: ‘Gwamnoni na shirin daukar fansa’

Majalisa za ta damka wa INEC ikon gudanar da zaben kananan hukumomi

Tsugunne ba ta kare ba duk da cewa Kotun Koli ta ba wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu a cewar Sunday Karimi.

Dan Majalisar Dattawan ya bayyana cewa wasu gwamnoni na shirin yadda za su wuce takaicinsu kan hukuncin kotun kotun koli da ya damƙa ikon gudanar da harkokin kananan hukumomi a hannun ciyamomi.

Sanata Sunday Karimi ya ce don haka Majalisar Dattawa za ta yi gyare-gyare a kundin tsarin mulki domin tabbatar da cewa gwamnoni suna biyayya ga umarnin kotun koli kan ’yancin kananan hukumomin.

Sanatan ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da majalisar za ta gyara a kansu a kundin tsarin mulki “akwai kwace ikon gudanar da zaben kananan hukumomi daga hukumomin zaben jihohi a dam a hannun Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

“Amma wasu gwamnoni za su yaki hakan.

“Shugaba Tinubu ya yi abin da ya dace wajen barin bangaren shari’a ya yi aikinsa, duk kuwa da cewa wa’adin farko na shugaban kasar ke nan ba tare da damuwa da batun sake neman tazarce a 2027 ba,” in ji shi.

A ranar Alhamis ne Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa saba wa dokar kasa ne rike kason kananan hukumomi na asusun kasa da gwamnatocin jihohi suke yi.

Kotun kolin ta kuma ba wa kananan hukumomi cikakken ’yancin gudanar da harkokinsu a hukuncin da ta yanke kan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar.

Sanata Karimi ya ce tun shekarar 1999 gwamnoni suka karbe wa kananan hukumomi ragana suka mayar da su tamkar wani sashe na gwamnatin jiha.

Don haka ya ce abin yabawa Tinubu ya yi.