✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan wasa 20 da ke sahun gaba wajen lashe kyautar Balon d’Or a bana

Akwai ’yan wasa 20 da ke kan sahun gaba wajen lashe kyautar Balon d’Or a bana.

A halin yanzu akwai ’yan wasa 20 wanda tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa a bana kuma suke kan sahun gaba wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Balon d’Or.

Jaridar wasannin kwallon kafa ta Goal.com da ake wallafawa a Intanet ce ta fidda jerin ’yan wasan a ranar Litinin.

Kididdigar da jaridar ta yi wa lakabi da Balon d’Or 2021 Power Rankings, ta ce bayan kammala dukkanin gasannin da ake bugawa a nahiyyar Turai kuma aka dirfafi gasar Euro 2020 da ta Copa America, wasu zaratan ’yan kwallon sun ci gaba da nuna kansu.

Ana iya tuna cewa, a bara wanda ya kasance karon farko a tarihi, ba a bayar da da kyautar zakaran dan kwallon kafa na duniya ba, saboda annobar Coronavirus.

Mujallar kwallon kafa ta Faransa wadda ke bayar da kyautar Balon d’Or duk shekara, ta ce babu yadda za a yi adalci wajen bayar da kyautar a bara ganin cewa akwai wasu kasashen da ba su kammala gasarsu ba.

Sai dai tun a baran Mujallar ta ce za ta mayar da hankali ne wajen shirya bikin da za a gudanar na bayar da kyautar a bana.

Dan wasan Argentina da ke murza leda a Barcelona, Lionel Messi ne ya lashe kyautar ta karshe da aka bayar a shekarar 2019, a yayin da Megan Rapinoe ta Amurka ta lashe kyautar a bangaren mata.

Kodayake, sai a watan Dasumba za a gabatar da kyautar ta bana, inda bajintar da ’yan wasan za su nuna a makonni masu zuwa ita ce za ta taka rawar gani wajen yanke hukunci a yayin fidda gwarzon dan wasa na bana.

Ga jerin ’yan wasa 20 da Jaridar Goal.com ta fitar tare da bajintar da suke ci gaba da yi a bana:

20. Luiz Suarez

Luis Suarez

Dan wasan kungiyar Atletico Madrid ya lashe gasar La Liga ta bana. Ya kuma jefa kwallaye 13 tare da bayar da taimakon wasu kwallayen biyu.

Idan kasarsa ta Uruguay ta yi wani katabus a gasar Copa America, hakan na iya tunkuda dan wasan zuwa sahun gaba-gaba na wadanda za su lashe kyautar Balon d’Or a bana.

19. Memphis Depay

Memphis Depay

Depay, sabon dan wasan da Kungiyar Barcelona ta siya daga Lyon, ya jega kwallaye 20 sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen 11 yayin kasancewarsa a Faransa.

Sai dai har yanzu dan wasan bai yi wata kwakkwarar bajinta ba ga tawagar kasarsa ta Netherlands yayin da take buga gasar Euro 2020.

18. Harry Kane

Harry Kane

Dan wasan na Kasar Ingila da kungiyar Tottenham, ya jefa kwallaye 19 da kuma taimakon wasu kwallayen biyar a bana.

17. Bruno Fernandes

Bruno Fernandes

Bajinta:Ya ci kwallaye 16 ya bayar da taimakon 10.

Kasa/Kungiya: Portugal/ Manchester United.

16. Mason Mount

Mason Mount

Bajinta: Ya jefa kwallaye 9, ya bayar da taimakon wasu uku. Ya ci kofin Zakarun Turai.

Kasa/Kungiya: Ingila/Chelsea

15. Ilkay Gundogan

Ilkay Gundogan

Bajinta: Ya zura kwallaye shida da taimakon wasu kwallayen shida a bana. Ya lashe kofin Firimiyar Ingila da kuma Carabao Cup.

Kasa/Kungiya: Jamus/ Manchester City

14. Frenkie de Jong

Frenkie de Jong

Bajinta: Ya zura kwallaye shida da taimakon wasu kwallayen shida a bana. Ya kuma lashe kofin Copa del Rey.

Kasa/Kungiya: Netherlands/ Barcelona

13. Antoine Griezmann

Antoine Griezmann

Bajinta: Ya jefa kwallaye 20, ya bayar da taimakon wasu 11. Ya ci kofin Copa del Rey.

Kasa/Kungiya: Faransa/ Barcelona

12. Neymar da Silva Santos Junior

Neymar

Bajinta: Ya jefa kwallaye 12 a koma sannan ya bada taimakon wasu kwallayen 9. Ya lashe kofuna biyu da suka hada da; Coupe de France da Trophees des Champions.

Kasa/ Kungiya: Brazil/ PSG

11. Erling Halaand

Erling Halaand

Bajinta: Ya jefa kwallaye 25 sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen 9. Ya lashe kofin DFB-Pokal.

Kasa/Kungiya: Norway/Dortmund

10. Phil Foden

Phil Foden

Bajinta: Ya jege kwallaye 11, ya bayar da taimakon wasu kwallayen bakwai. Ya lashe kofin Firimiyar Ingila da Carabao Cup.

Kasa/Kungiya: Ingila/ Manchester City

9. Karin Benzema

Karin Benzema

Bajinta: Ya zura kwallaye 18 a koma, ya kuma bayar da taimakon wasu kwallayen biyar a bana.

Kasa/Kungiya: Faransa/ Real Madrid

8. Ruben Dias

Ruben Dias

Bajinta: Ya ci kwallo daya. Ya lashe kofin Firimiyar Ingila da Carabao Cup. Dan wasan bayan ya yi wasanni 19 ba tare da an jefa kwallon a komar da yake tsaro ba.

Kasa/ Kungiya: Portugal/ Manchester City.

7. Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo

Bajinta: Dan wasan ya jefa kwallaye 25 sannan ya bayar da taimakon wasun kwallayen hudu. Ya lashe gasar Coppa Italia da Supercoppa Italiana.

Ronaldo ya jefa kwallaye uku a wasanni biyun farko da ya haska a gasar Euro 2020.

Kasa/Kungiya: Portugal/ Juventus

6. Lionel Messi

Lionel Messi

Bajinta: Messi ya zura kwallaye 30 a bana sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen goma. Ya lashe gasar Copa del Rey.

Kasa/Kungiya: Argentina/Barcelona

5. Romelu Lukaku

Romelu Lukaku

Bajinta: Lukaku ya jefa kwallaye 20 a kakar wasannin bana tare da bayar da taimakon wasu kwallayen bakwai. Ya kuma lashe gasar Serie A.

Kasa/Kungiya: Belgium/Inter Milan.

4. Robert Lewandowski

Robert Lewandowski

Bajinta: Dan wasan ya zira kwallaye 32 a bana sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen hudu. Ya lashe gasar Bundes Liga da Club World Cup.

Kasa/Kungiya: Poland/Bayern Munich.

3. Kevin Debryune

Kevin Debryune

Bajinta: Ya jefa kwallaye 10 sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen 9 a bana. Ya lashe gasar Firimiyar Ingila da Carabao Cup.

Kasa/Kungiya: Belgium/Manchester City

2. Kylian Mbappe

Kylian Mbappe

Bajinta: Mbappe ya zira kwallaye 29 a koma sannan ya bayar da taimakon wasu kwallayen biyar. Ya lashe gasar Coupe de France da kuma Trophee des Champions.

1. Ngolo Kante

Ngolo Kante

Bajinta: Ya bayar da taimakon kwallo daya sannan ya lashe gasar Champions League.

Kante ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da Chelsea ta lallasa Manchester City, da kuma wasannin kusa daf da na karshe a gida da waje na gasar da Chelsea ta lallasa Real Madrid.

Kasa/Kungiya: Faransa/Chelsea