Babu sunan Lionel Messi a cikin jerin zaratan ’yan wasan kwallon kafa da ke takarar lashe kyautar Balon d’Or ta bana.
Messi wanda ya lashe kyautar har sau bakwai ya gamu da koma-baya sakamakon rashin sanya sunansa a cikin jerin zaratan ‘yan wasa 30 da ke takarar lashe kyautar da ake bai wa dan wasa mafi nuna hazaka a shekara.
Messi da ya sauya sheka daga Barcelona zuwa PSG da taka leda, tun shekara ta 2006 yake shiga cikin jerin ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar, yayin da a bara aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe kyautar.
Kazalika tun shekara ta 2007, yake shiga cikin jerin ‘yan ukun farko da ke takarar lashe kyautar, in ban da shekara ta 2018.
Sai dai a bana, Messi mai shekaru 35, bai samu shiga cikin ‘yan takarar ba, la’akari da rashin katabus da ya yi a duniyar kwallon kafa.
Kazalika, sauyin da aka kawo wajen zakulo zaratan ‘yan wasan, shi ma ya kawo cikas ga Messi din, inda a yanzu aka daina la’akari da rawar da dan wasa ya taka a tsawon shekara guda, a maimakon haka, yanzu ana duba bajintar dan wasa ne a cikin kaka guda.
Tun dai da ya koma PSG daga Barcelona, dan wasan ya gaza nuna wata bajintar a-zo-agani a kungiyar ta Faransa wadda ke kishirwar lashe kofin gasar zakarun Turai. Hasali ma kwallaye 11 ya iya zurawa a raga a PSG din.
A ranar 17 ga wannan wata na Agusta ne za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan na bana a birnin Paris na Faransa.
Karim Benzema dai, shi ne kan gaba a jerin ‘yan wasan da hasashe ke nuna cewa, za su iya lashe kyautar ta Balon d’Or a bana, ganin yadda ya taimaka wa Real Madrid wajen lashe gasar Zakarun Turai da ta gabata.
Kazalika, akwai Cristiano Ronaldo na Manchester United da shi ma ke cikin masu takarar a bana, wanda jaridar L’Equipe ta tabbatar da cancantar shigarsa karo na 18 ke nan a jere babu fashi.
Jaridar ta ce Ronaldon ya taka rawar gani a United, wanda kwallaye 6 da ya ci ya kai kungiyar zagayen ’yan 16 a gasar Zakarun Turai. Haka kuma dan wasan ya ci kwallaye 32 cikin wasanni 49 da ya buga a kakar da ta gabata.
Ga dai jerin ’yan wasa 30 masu takarar lashe kyautar Balon d’Or ta bana:
- Karim Benzema, (Real Madrid)
- Thibaut Courtois, (Real Madrid)
- Vinicius Junior, (Real Madrid)
- Casemiro, (Real Madrid)
- Luca Modric, (Real Madrid)
- Antonio Rüdiger, (Real Madrid)
- Mohammed Salah, (Liverpool)
- Trent Alexander-Arnold, (Liverpool)
- Luis Díaz, (Liverpool)
- Fabinho, (Liverpool)
- Darwin Núñez, (Liverpool)
- Vigil Van Dijk, (Liverpool)
- Riyad Mahrez, (Manchester City)
- Bernardo Silva, (Manchester City)
- Phil Foden, (Manchester City)
- Kevin De Bruyne, (Manchester City)
- Joao Cancelo, (Manchester City)
- Erling Haaland, (Manchester City)
- Robert Lewandowski, (Barcelona)
- Heung-Min Son, (Tottenham)
- Karry Kane, (Tottenham)
- Joshua Kimmich, (Bayern Munich)
- Sadio Mané, (Bayern Munich)
- Leao, (AC Milan)
- Mike Maignan, (AC Milan)
- Nkunku, (Leipzig)
- Cristiano Ronaldo, (Manchester United)
- Kylian Mbappe, (PSG)
- Haller, (Borussia Dortmund)
- Dusan Vlahovic, (Juventus)