Ɗan wasan gaban ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid bayan ya raba gari da PSG.
Tun a watan Fabrairu, Mbappe ya yanke shawarar koma wa Real Madrid da taka leda.
- Dalilin da sojoji ke samun nasarar juyin mulki — Janar Abdulsalami
- Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai karo na 15
Wannan dai na zuwa ne bayan Real Madrid ta kafa sabon tarihi a Gasar Zakarun Turai, bayan doke Dortmund da ci 2 da nema a wasan ƙarshe na gasar a daren ranar Asabar.
Real Madrid ta shafe tsawon shekara huɗu tana zawarcin ɗan wasan amma PSG ta ƙi sayar da shi, lamarin da ya sanya alaƙa ta yi tsami tsakanin ƙungiyoyin biyu.
Sai dai duk da haka, Mbappe ya amince ya koma Madrid ne, domin cikar burinsa na yarinya wanda ke son ganin ya sanya wa ƙungiyar riga.
Ɗan wasan ya sanya hannu kan duk wasu takardu da suka shafi kwantaraginsa da Real Madrid.
A makon da za a shiga ne ake sa Real Madrid za ta sanar da ɗaukar ɗan wasan daga PSG a hukumance.