A ranar Lahadin da ta gabata ce aka kammala gasar cin Kofin Nahiyar Turai na bana (EURO 2020), inda kasar Italiya ta yi galaba a kan Ingila da ci 3-2, a bugun finareti, bayan sun tashi wasan kunnen doki – 1-1.
Kafofin sada zumunta na zamani sun karade duniya da cin mutunci ta hanyar bayyana tarzomar da mutanen Ingila suka yi a kan magoya bayan Italiya da sauran wadanda ba ’yan kasar Ingila ba a filin wasan.
Akwai kuma kalaman nuna wariyar launin fata wadanda ake zargin magoya bayan Ingila da yi wa ’yan wasa da suka hada da Jadon Sancho da Marcus Rashford da Bukayo Saka, wadanda suka yi barin bugun finareti a wasan na ranar Lahadi.
Idan aka kwatanta hakan da gasar wasan kwallon kafa a Najeriya, za a iya cewa sammakal ne ba ya da bambanci da abin da yake faruwa na rashin da’a da magoya baya suke nunawa wajen ta da tarzoma da aka saba yi.
Cikin irin wannan tarzoma ta nan cikin gida akwai kakar wasanni ta bana da aka yi hayaniyar magoya baya a tsakanin Remo Stars da Bendel Insurance sai tsakanin Plateau United da Enyimba; kana na Kano Pillars da Akwa United.
Sai dai dan bambancin kawai da za a iya cewa shi ne na tasirin jaridu wajen yada batun wanda kafofin labaran Ingila a nasu bangaren suka yi kokarin dakile batun – suka yi matukar sirranta munanan lamuran kasar.
Godiya ga muhimmiyar rawar da kafofin sada zumunta na zamani suke takawa wajen bayyanar da ireiren wadannan batutuwa.
Wani dan jarida a Kano kuma mai sharhi a kan wasan kwallon kafa, Aminu Halilu Tudun Wada ya tattauna da Aminiya kan batun tarzoma da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Ingila.
A cewarsa, ba boyayyen abu ba ne nuna tsageranci da rashin da’a da magoya bayan kasar Ingila suka yi ga ’yan wasan kasar bakaken fata da magoya bayan abokan hamayya.
Yunwar kofi da tarihin tarzomar magoya baya
Dan jaridar ya ce tsageranci da rashin da’a na magoya bayan Ingila sun kara bayyana a wani faifan bidiyon da ya karade duniya.
A cikin faifan, an nuno magoya bayan Ingila suna duka da cin zarafin magoya bayan kasar Italiya.
Wannan ba shi ne farau ba kasancewar sun yi makamancin wannan na yin ihu ga taken kasar Denmark, a wasan kusa da na karshe da Ingila ta buga da Denmark.
Sannan kuma a wasan ne magoya bayan Ingila suka rika haska fitila a idanun mai tsaron gidan Denmark, Kasper Schmeichel, ana dab da Harry Kane zai buga finareti.
“Dama can tarihi ya nuna Ingila ta yi kaurin suna a harkar ta da husuma da tarzoma daga magoya baya.
A 2016 magoya bayan Ingila sun ta da tarzoma a tsakaninsu da ’yan sanda a Faransa.
Sannan sun yi husuma da magoya bayan kasar Rasha, a gasar Euro ta 2016.
“A shekarar 2019, a gasar Kofin Turai na Nations League da aka buga a kasar Portugal, sai da ta kai ga aka bai wa ’yan makaranta hutu sakamakon hatsaniyar magoya bayan Ingila.
“Haka zalika, magoya bayan Ingila sun ta da hatsaniya a gasar Euro ta 2000, a birnin Charleroi na kasar Beljiyum jim kadan bayan rashin nasarar da Ingila ta yi a hannun Portugal a gasar,” inji dan jaridar.
“Tasirin jaridun Ingila ya sanya magoya baya suke da yakini da zumudin nasara a wasan karshen lura da yadda suke yunwar kofin inda kasar ta shafe shekara 55 ba tare da lashe duk wani kofi ba.
“Hakan ne ya sa jaridun suka kirkiri taken ‘It’s Coming Home’, ma’ana kofin zai taho gida inda asalin kwallon kafa ta samu asali, wanda rashin samun nasarar da aka kamba ya yi tasiri kwarai wajen kara harzuka magoya bayan su tayar da tarzoma.”
Sakacin jami’an tsaro
Mai sharhin ya ce akwai sakaci wajen daukar matakan riga-kafi daga jami’an tsaro na Ingila lura da cewa suna sane da wadanda suke ta da zaune-tsaye a filayen wasannin kasar.
“Za mu iya cewa su ma jami’an tsaro da sakacinsu saboda sun san irin al’ummarsu da halayensu.
“Ya kamata a ce sun dauki matakan dakile aukuwar haka, ta hanyoyi da dama, kamar yadda suka yi a shekarun baya suka hana wadansu fitattu da suka yi kaurin suna wajen ta da zaune-tsaye zuwa kasashen ketare a manyan gasanni don dakile wannan matsala.
“Sai dai wannan karon sun yi sakaci, hakan ya shafa musu bakin fenti tare da fama tsohon ciwon da kasar ta haifar wa kasashe da dama a harkar kwallo,” inji shi.
Ba ta tsaya ga wasannin kasashe ba
Lamarin bai tsaya ga wasannin ayarin kwallon kafa na kasar kawai ba, kamar yadda dan jaridar ya nuna: “Wasannin hamayya kamar a tsakanin Tottenham da Arsenal ko Liverpool da Everton ko Manchester United da Manchester City, suna daga cikin wasannin da ake yawan samun hatsaniya da tarzoma a tsakanin magoya baya da suke da mabambantan ra’ayoyi a Ingila.
“Tarihi ba zai manta da ‘Heysel Disaster’ ba, lokacin wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai a 1985, inda magoya bayan Liverpool dalilin hatsaniya a tsakaninsu da magoya bayan Juventus suka haddasa rushe gini a filin wasa inda ya danne tare da kashe magoya bayan Jubentus 39 a brinin Brussels na kasar Beljiyum,” inji shi.
Tarihi ya nuna cewa wannan mummunar dabi’a ta magoya baya ba ta tsaya a kan magoya baya a Ingila kadai ko kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.
Faransa da Portugal da Spain da Italiya duk sun sha fama da matsalar nuna wariyar launin fata, sai dai sun yi kokarin takaita aukuwar haka a kasashensu, inda hakan ya sa ba kasafai akan samu tashe-tashen hankali kamar yadda magoya bayan Ingila suke yi ba.
Yanzu dai a iya cewa kallo ya koma sama inda za a yi dakon hukuncin da kasar Ingila za ta dauka ko matakan da za ta fito da su wajen kawo karshen wannan kashin kaji da magoya bayanta suka yi kaurin suna a fadin duniya wajen shafa mata