Tawagar ‘yan wasan kasar Ukraine sun taka muhimmiyar rawa a gasar kofin Europe 2020 da aka kammala a watan da ya gabata, amma hakan bai hana kocinta Andriy Shevchenko ajiye aikinsa ba.
Shevchenko ya sanar da ajiye aikin nasa bayan shafe shekara biyar ya jagorancin ‘yan wasan kasar, bayan karewar kwantaraginsa.
- Taliban ta kai hari filin jirgin saman Kandahar a Afghanistan
- Za a yi wa yara miliyan 1.7 rigakafin shan-inna a Jigawa
A ranar Lahadi ce tsohon dan wasan gaban kungiyar AC Milan, ya sanar da cewa ba zai sabunta kwantaraginsa da tawagar ‘yan wasan kasar ba cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.
“Yau kwantaragina da Hukumar Kwallon Kafa ta Ukraine ya kare.
“Na shafe shekara biyar inda muka yi aiki tukuru kuma wannan ya nuna za mu iya buga kwallon zamani kamar kowace kasa.
“Dukkaninmu mun nuna cewar za mu iya kai wa wani mataki a kwallon kafa a yanzu,” a cewar sakon.
Shevchenko ya fara aiki ne a matsayin mataimakin mai horas da tawagar ‘yan wasan a 2016.
Daga bisani ya karbi ragamar kocin ‘yan wasan har ga kai su ga wasan kusa da na karshe a gasar Euro 2020, wanda shi ne karo na farko da kasar ta taba zuwa a tarihinta.