Tun farkon fara Gasar Euro ta bana, shafin Bakin Raga ya zauna da masu sharhin wasanni, Mubarak Abubakar da Salisu Musa Jegus da Isiyaku Muhammed, inda muka yi hasashen kasashen da za su iya lashe gasar ta bana.
Tun a lokacin, Mubarak ya yi hasashen cewa Italiya ce za ta lashe gasar.
Wannan ya sa Bakin Raga ya koma gare shi domin jin me yq hango da tun a farkon gasar ya yi wannan hasashen.
Ga abin da ya ce:
“Tun kafin a fara wannan gasa da aka kammala, na yi hasashen cewa kasar Italiya za ta cinye kofi.
Shikashikan nasara
“Na yi hakan ne duba da cewa a gasa irin wannan, akwai wasu abubuwan dubawa da ya kamata kasar da ke son samun nasara ta tara su, irin samun ’yan baya gogaggu, gola zakakuri mai kwarjini da jan ragamar ’yan wasa a fili kuma mai iya shirya tsayuwar ’yan baya ya musu magana.
“Sannan ta kasance tana da ’yan tsakiya da suke da wayo, dabara da kuma kwarewa a kafarsu.
“A bangaren ’yan gaba ta samu wadanda za su iya cin ball daga kowace kusurwa ba sai an shiga yadi na 18 ba.
“A karshe ya kasance akwai mai horaswa gogagge.
“Da na yi duba na tsanaki, sai na ga cewa kasar Italiya ita ce wacce ta fi kowace cika wadannan sharuddan.
Matashin gola
“Golansu Donnarumma ya fi kowane gola kyau a yanzu, a cikin masu tsaron gida da suka halarci wannan gasa.
“Tun kafin gasar, a shekara biyar da ya yi da fara kama wa kasarsa gola, ba a taba zura masa kwallo sama da daya ba.
“Dangane da shi golan nasu dai, duk da karancin shekarunsa, ya saba jagoranci a kulob dinsa, AC Milan; wannan ya taimaka masa wajen hada kan ’yan baya, kuma ya agaza wa sauran ’yan wasan a inda sauran suka gaza.
“Batun ’yan baya kuwa, Italiya sun zo da Chillieni da Bonucci, ’yan bayan da suka fi dadewa suna buga kwallo tare a gasar.
“Bugu da kari, abin da zai kara nuna ma kyawun bayan Italiya din shi ne, tun kusan karshen shekarar 2018 har lokacin da za a fara Euro ba a yi nasara a kansu ba.
“A bangaren tsakiyar fili kuwa, gogewar Verratti, iya rike ball ya raba, ga Jorginho, da kuma kokari na Barella, wanda shi ne aka zaba a matsayin dan tsakiya da ya fi kowa bajinta a kakar Serie A da ta gabata, ba karamin kara daure tsakiyar Italiya ya yi ba.
“Hakan ya sa tsakiyar tasu takan iya sauya salon wasa daga tarewa (idan sun hadu da wadanda suka fi su iya rike ball kamar Spain), zuwa tattaba ball a rike (kamar yadda suka yi wa Belgium da Ingila).
“Dangane da ’yan gabansu kuwa, Inisigne, Berrardi, Chiesa duk suna iya cin ball daga kowace kusurwa ba sai an shiga yadi na 18 ba.
“Hakan ya ba su gudunmawa sosai, sai kuma gogewa irin ta Immobile yadda yake iya gwagwarmayar daukar ball din sama a tsakankanin ‘yan baya.
Tasirin Mancini
“Abu na karshe shi ne kocinsu Mancini. Shi dai ya kasance koci mai gogewa tun daga lokacin da ya ci Serie A sau biyu da Inter Milan, ya kuma shigo Ingila ya ci wa Manchester City Firimiyarsu ta farko, da kuma Kofin Kalaubale wato FA Cup wanda hakan ne ya dora su a kan turba.
“Daga cikin kwazonsa, tun da ya karbi Italiya bayan sun kasa zuwa Gasar Cin Kofin Duniya a 2018, shekara uku ke nan ba wanda ya yi nasara a kansa.
“A kaf gasar Euro, babu wani mai horaswa da ya kai shi gogewa a harkar koci.
“Wadannan abubuwan da na zayyana su ne suka sa na ce Italiya za ta cinye gasa, ga shi kuma cikin ikon Allah hakan ya tabbata.”