✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan tseren Rasha sun yi zanga-zangar yunkurin hana su yin auren jinsi

Wasu ’yan matan Rasha da suka fafata a tseren gasar wasanni ta duniya da aka kammala a karshen makon nan a Mosko masu suna Kseniya…

Masu zanga-zangar hana auren jinsi a RashaWasu ’yan matan Rasha da suka fafata a tseren gasar wasanni ta duniya da aka kammala a karshen makon nan a Mosko masu suna Kseniya Ryzhoba da Tatyana Firob sun yi zanga-zangar neman hana su yin auren jinsi a yunkurin da majalisar dokokin kasar ke neman zartarwa a kan hana auren jinsi.
Matan, wadanda suka lashe lambar zinare a fafatawar da suka yi a gasar tseren da ake wa lakabi da IAAF track championships in Moscow da aka kammala a ranar Lahadin da ta wuce a mataki na ’yan hurhudu bangaren mata a gudun mita 400 (4d400m) sun bayyana bacin ransu ne ta hanyar sumbantar juna a bainar jama’a ba tare da nuna shakka ko kunya ba.
Ita dai majalisar dokokin Rasha tana yunkurin hana auren jinsi ne a wani kudurin dokar da ke gabanta a halin yanzu da hakan bai yi wa masu madigo maza da mata dadi ba.