✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan tawayen Houthi sun kai wa jiragen ruwan Amurka da Birtaniya hari

Wani kamfanin tsaro mai suna Ambrey ya sanar cewa jirgin Birtiyan da aka kai wa harin na dakon kaya ne

’Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kai wa jiragen ruwan Amurka da Birtaniya hare-hare a ranar Talata a Tekun Bahar Maliya.

Kakakin kungiyar ’yan tawayen na Houthi, Yahya Saree ya ce, “harin farko an kai shi ne kan jirgin Amurka mai suna Star Nasia, na biyun kuma a kan jirgin Birtaniyai mai suna Morning Tide.”

Ya ci gaba da cewa ’yan Houthi, “za mu ci gaba da kai hare-haren a kan Amurka da Birtaniya domin kare kanmu,” in ji shi a kafar X, a ranar Talata.

Wani kamfanin tsaro mai suna Ambrey ya sanar cewa jirgin Birtiyan da aka kai wa harin na dakon kaya ne kuma harin ya yi masa barna, amma bai yawa ba.

Hukumar kula da lafiyar teku ta Birtaniya (UKMTO) ta ce an kai wa jirgin ruwan hari ne a yankin Hodeida.

’Yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran kuma suke iko da kasar Yemen, ta sha kai hare-hare a Tekun Bahar Maliya domin nuna adawarsu ga kisan gillar da Isra’ile ke yi wa Falasdinawa a Gaza.

Hare-harensu kan jiragen ruwan kasashen da ke goyon bayan Isra’ila na shan suka, kuma sun jawo harin ramuwar gayya daga sojin kasashen biyu a ranar Asabar.