✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’addan Neja-Delta sun ayyana dakatar da kai hare-hare

kungiyar Niger Delta Abengers (NDA),  da ke fasa bututun mai a yankin Neja-Delta ta ayyana dakatar da kai hare-hare a yankin.Wata sanarwa da ta fito…

kungiyar Niger Delta Abengers (NDA),  da ke fasa bututun mai a yankin Neja-Delta ta ayyana dakatar da kai hare-hare a yankin.
Wata sanarwa da ta fito daga kungiyar mai taken: “Budaddiyar Wasika zuwa ga Shugaban kasa,” ta ce, tana fatar “samun wani hali nagari na sake fasalin kasa da bayar da ’yanci ga kowane bangare na Najeriya.”
Sanarwar ta kungiyar Abenger wadda kamar martani ne ga bayanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar Kenya na cewa gwamnatin Najeriya za ta sanya kafar wando daya da ’yan ta’addan Neja-Delta kamar yadda ta yi da ’yan Boko Haram matukar suka ki amincewa da batun sulhu. Sai dai NDA ta bugi kirji cewa duk dimbin sojojin da za a tura yankin ba zai sa Shugaban kasar ya samu nasarar yaki a yankin mai albarkatun man fetur.
Ta ce, kalaman na Shugaba Buhari da yadda sojojin suke kara karfi a yankin Neja-Delta alama ce ta cewa sojojin babu abin da suka iya face yin kisan kare-dangi a yankin.
 “Sojojinka suna yunkurin aiwatar da kisan gilla a yankin Neja-Delta abin da ya saba wa doka ta 4 ta taron Geneba ta hanyar shirinsu mai taken: “Operation Crocodile Smiles.” Sanarwar ta kada da cewa duk wani mai hankali ya sana ma’anar ‘hawayen kada,’ don haka sanya wa shirin ‘murmushin kada,’ ya nuna mugun shirinka ga duniya kan yankin Neja-Delta.
kungiyar dai ta rika daukar alhakin ayyukan fasa bututun man fetur da na gas a yankin, inda take ikirarin tana yin haka ne domin a kara wa yankin kaso daga kudin man da ake hakowa. barnar hare-harenta ya jawo koma-baya wajen hakowa da fitar da mai daga kasar nan da kimanin ganga dubu 700 a kullum daga cikin ganga miliyan biyu da dubu 200 da take hakowa a matsayinta na kasa mafi fitar da man a Nahiyar Afirka.