Gwamnatin Adamawa ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa’o’i 24 a Karamar Hukumar Lamurde da ke Kudancin jihar.
Bayanai sun ce wannan lamarin na zuwa ne bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci da ya auku a yankin.
- Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil
- Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC
DW ta ruwaito kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje yana ba da shaidar matakan da suke dauka domin dakile rikicin.
Kazalika Kwamishin ’yan sandan jihar, Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.
Kana Kwamishinan ya ba da umarnin jibge ’yan sandan kwantar da tarzoma a yankin na Lamurde domin tabbatar da doka da oda.
Ko a farkon wannan wata na Yuli da muke ci, an samu tashin hankali a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar ta Adamawa.