Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa.
Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata.
A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji.
Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari.
“Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin an kawo ƙarshen wannan hare-hare a yankin,” in ji shi.
Yohanna ya bayyana damuwa kan yadda mayaƙan Boko Haram ke ci gaba da ƙara ƙarfi a bayan nan da ke zama abin fargaba ga mazauna yankunan da abin ya shafa.
“Mun samu labarin cewa wani jirgi mai saukar ungulu ne yake jigilar mayaƙan daga sansaninsu zuwa wuraren da suke sheƙe ayarsu ba tare fuskantar wata tirjiya ba.
“Amma ina mai tabbatar da cewa muddin Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki ta hanyar tanadar makamai na zamani, za a kawo ƙarshen waɗannan maƙiya cikin lokacin ƙanƙani.”
Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta tanadar wa mafarauta da ’yan sa-kai manyan makamai na zamani domin kawo ƙarshen mayaƙan Boko Haram a yankin.
Wannan harin dai na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 12 da wasu ’yan ta’adda suka kashe fiye da mutum 30 ciki har da mata da ƙananan yara a ƙananan hukumomin Kala Balge da Gambarou Ngala da ke jihar.