’Yan ta’adda sun yi awon gaba da matafiya da ba a tantance adadinsu ba a hanyar Katsina zuwa Jibia a Jihar Katsina.
Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa maharan da ke kan babura sun yi ta luguden wuta sannan suka yi awon gaba da matafiya cikin wasu motoci biyu a daidai kauyen Kadobe a yammacin ranar Laraba.
- Gwamnati za ta ba da kwangilar tsaron Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
- EFCC ta titsiye Daraktan NDDC kan zargin badakalar N25bn
Shaidun sun ce ’yan bindigar, “Ba su fi su 20 ba kuma ba su sa shinge ba, tsayawa suka yi kawai a gefen hanya suka yi ta harbe-harbe.
“Hakan ne ya yi sanadiyyar motoci biyu suka kwace suka sauka daga kan hanya, su kuma maharan suka tarkata mutanen cikinsu suka tafi da su,” in ji wani ganau.
Ya yi zargin cewa an sanar da jami’an tsaro a lokacin da abin ke faruwa, amma ba su iso ba sai bayan kimanin rabin awa da tafiyar maharan.
A baya-bayan nan dai ’yan ta’adda sun matsa da hare-hare a kan hanyar Katsina zuwa Jibia, duk kuwa da yawan shingayen bincike na jami’an tsaro da kuma barikin sojoji da ke kan hanyar.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani gam da abin da ya faru amma har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto, kakakin ’yan sandan Jihar Katsina bai sauki kiransa ba.