Hedkwatar Rundunar Sojojin Kasa Najeriya ta ce ‘yan ta’adda 4,770, maza da mata ne suka mika wuya ga sojoji a cikin makonni biyun da suka gabata.
Hedkwatar ta ce, daga cikin ‘yan ta’addan akwai maza manya 864 da mata 1,415 da kuma kananan yara 2,490.
- An yi bikin rada wa Amurkawa 40 sunayen gargajiyar Ibo a Enugu
- Alhajin Sakkwato ya mayar da sama da N400,000 da ya tsinta a Madina
Daraktan Yada Labarai na Rundunar, Manjo-Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ofishin ya gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce wannan ya faru ne a shiyyar Arewa maso Gabas, tsakanin daya zuwa 15 ga watan Yunin 2022.
Jami’in ya ce, wannan nasarar ta samu ne sakamakon ninka kokarinsu da dakarun Operation Hadin Kai suka yi wajen yaki da ta’addanci a sassan shiyyar Arewa maso Gabas.
Kazalika, ya ce kokarin dakarun ya taimaka wajen kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su da kashe ‘yan ta’adda da dama tare da damke wasunsu, kwato bindigogi da alburusai da dai sauransu.
A cewar Onyeuko, a tsakanin 17 da 21 ga Yuni, dakarun Bataliya ta 152 sun yi arangama da mayakan Boko Haram/ISWAP a yankin Buduwa cikin Karamar Hukumar Bama, Jihar Borno, inda suka sheke bakwai daga cikin ‘yan ta’addar.
Ya ce sun kwato shanu 14 da babura 3 daga hannu ‘yan bindigar, kana sun damke wasu da suke taimaka wa mayakan wajen gudanar da harkokinsu.
Ta bakin jami’in, an damke Malam Abacha Usman ne a Benshek, sannan aka kama Malam Ibrahim Gira a hanyar Damboa zuwa Biu, haka shi ma Malam Ibrahim Gira wanda ya gawurta wajen saida wa mayakan fetur ya fada a jami’an tsaron.
Ya ce ‘yan ta’adda 11 sojojin suka halaka, sannan sun kama 11 tare da kwato shanu 14 da bindiga kirar AK47 biyu da kekuna uku da kananan motoci biyu da sauransu.
“Baki dayan wanda suka mika wuyan, an dauki bayanansu yadda ya kamata, sannan an mika wadanda aka damke da kuma kayayyakin da aka kwato ga hukumar da ta dace,” inji shi.
(NAN)