A yayin da ake shirin yin zabe a Jihar Uttar Pradesh da ke kasar Indiya sun fara kamfen din neman kuri’ar jama’a ta hanyar nada wa karnuka fostocin neman zabensu su yi yawo da su, domin nema musu magoya baya da yawa.
Akalla ’yan takara biyu ne suka yi hakan, daya daga birnin Rae Bareli, dayan kuma a gundumar Ballia inda suka rataya wa karnuka fostocin neman takararsu suna yawo da su.
Hotunan karnukan nata yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani a karshen mako, yayin da masu kare hakkin dabbobi suke yada hotunan a shafukan intanet.
Duk da tsokacin da wasu ke yi wa ’yan takarar kan fallasa manufofinsu a jikin karnukan, wani dan takarar wanda aka yi amfani da fostarsa a jikin karnukan ya ce bai yi nadamar hakan ba.
“Ba wata doka da ta hana mu yin amfani a karnukan da ke gararamba a hanya mu yi a kamfe da su.
“Ba ma cutar da dabbobin ta kowace hanya,” inji dan takarar wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
“Muna ciyar da karnukan kullum. Wannan labari ne mai kyau sannan yana daukar hankalin masu zabe.”
Masu kare hakkin dabbobi da masoya karnuka ba su amince da bukatar karnukan ba.
Mafi yawan su suna amfani da karnukan ne a matsayin allunan yada manufofinsu, akwai bukatar a hukunta su.
“Ya mutum zai ji a ransa idan aka manna masa wani allon talla a fuskarsa a lokacin zabe?” cewar wani mai kare hakkin dabbobi mai suna Reena Mishra.
“Saboda karnuka ba za su iya yin zanga-zanga ba, bai kamata a rika yin amfani da su ta wannan hanyar ba.
“Ya kamata ’yan sanda su dauki mataki kan ’yan takarar da ke aikata irin wannan,” inji shi.