✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sandan Kebbi sun kama ’yan fashi da masu satar mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 10 kan zarginsu da yin fashi da makami da satar mutane. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Ibrahim…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 10 kan zarginsu da yin fashi da makami da satar mutane.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Ibrahim M. Kabiru ya bayyana haka ga manema labarai lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai a Hedikwatar ’Yan sanda jihar da ke Birnin Kebbi, inda ya ce rundunarsa ta lashi takobin ci gaba da dakile ayyukan miyagu a jihar.

Kwamishinan ya ce zai dauki matakin da ya kamata domin kara wa jami’ansa kwarin gwiwa wajen samar da yanayin da mutanen jihar za su samu damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

Alhaji Ibrahim Kabiru ya ce, daga lokacin da aka kawo shi Jihar Kebbi ya lashi takobin sa kafar wando daya da masu tayar da zaune-tsaye, inda ya yaba hadin kan da kungiyoyi da daidaikun jama’a ke ba rundunar, kuma ya nemi jama’a su ci gaba da samar da bayanan da za su sa a dakile miyagun da ke barazana ga rayuwar jama’a.

Kwamishinan ya ce cikin wadanda aka kama akwai Mohammed Altine Babuje da Umaru Sajo da Mohammed Nasamu da Shu’aibu Abubakar da Sadik Usman da Babangida Jega, wadanda aka kama su da bindigogi da alburusai a garurukan Bunza da Tungar Bello da Burbuje da Jega da Masama.

Ya ce sauran mutanen su ne suka sace Limamin Senchi, Alhaji Mode Senchi a bara, amma ba a kama su ba sai a kwanan nan. 

Kuma ya ce rundunarsa, ta yi karin girma ga ’yan sanda766, 181 sun samu karin girma daga Saje zuwa Sufeto, sai 585 daga Kofur zuwa Saje.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu kan taimakon da yake ba su a matsayinsa na shugaban tsaro a Jihar Kebbi.