✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan sandan Kano sun kame dan sandan da ya harbe matashin da ke karatun likita

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kame dan sandan da ake zargi da harbe wani matashi mai suna Zaharadeen Sammani wanda ke karatun…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kame dan sandan da ake zargi da harbe wani matashi mai suna Zaharadeen Sammani wanda ke karatun likita a kasar Indiya.

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan a Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa Aminiya cewa dan sandan da ake zargi yana tsare a hannun Rundunar ‘yan sanda.” Bayan kama dan sandan zamu tabbatar da an yi adalci.” In ji shi.

Matashin Zaharadeen, ya gamu da ajalinsa ne bayan da takaddama ta barke a tsakaninsa da Dan sandan wanda ya harbe shi a kirji a daura da hotel din Royal Tropicana da ke kan titin Niger a Kano  a ranar Larabar da ta gaba ta, a lokacin a aka garzaya da shi asibiti a nan Allah Ya karbi ransa.