Hafsoshin ’Yan sanda 12 da aka yi garkuwa da su a titin Kankara zuwa Sheme a Jihar Katsina mako biyu da suka gabata sun kubuta kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.
An rawaito cewa an garzaya da ’yan sandan zuwa wani babban asibiti a birnin Gusau, Jihar Zamfara don duba lafiyarsu.
- Da zarar an janye yajin aiki za a rubuta jarabawa —ASUU
- An sace Shugaban Karamar Hukuma da wasu mutum 13 a Edo
- ’Yan bindiga: Gwamnatin Kaduna ta ziyarci kauyukan hanyar Abuja
Wakilinmu ya tuntubi Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, Usman Nagogo, sai ya sada shi da Kakakin Rundunar na Kasa, Frank Mba.
“Ka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sanda na kasa saboda lamarin an mika shi zuwa shelkwatar ’yan sanda ta kasa”, Inji Nagogo.
Frank Mba, ya tabbatar cewa tara daga cikin jami’an sun kubuta daga hannun masu garkuwar.
An dai yi garkuwa da hafsohon ’yan sandar ne a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Zamfara don gudanar da wani aiki na musanman.
Wata majiya ta ce sai da masu garkuwar suka bukaci kudin fansa kafin su saki jami’an ’yan sandar.