✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno

An haramta amfani da sinadarin urea a jihohi da dama ciki har da Jihar Borno, saboda yadda 'yan ta'adda ke amfani da su wajen ƙera…

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025.

Rundunar kai ɗaukin gaggawar (RRS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishin ‘Yan sandan jihar CP Yusufu Mohammed Lawal ne ta kama waɗanda ake zargin a ranar 13 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a unguwar Tashan Journey, Maiduguri.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Shamsuddeen Rabiu mai kimanin shekara 35, Malam Yau mai shekara 29, da Ibrahim Mohammed Sani mai shekara 30, suna jigilar takin zamanin da aka haramta samfurin urea ne, a cikin buhun taki na NPK a cikin keke NAPEP mai lamba GZA 17 ƁH Borno.

Rundunar ’yan sandan ta jaddada cewa, an haramta amfani da sinadarin urea a jihohi da dama ciki har da Jihar Borno, saboda yadda ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen ƙera ababen fashewa.

Yanzu haka dai waɗanda ake zargin suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi akan su.

Rundunar ’yan sandan jihar ta jaddada ƙudirinta na tabbatar da tsaro da tsaron al’ummar Jihar Borno, sannan ta buƙaci jama’a da su guji yin mu’amala da haramtattun abubuwa.