Babban Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya ƙaddamar da Ƙwararrun Jami’an tsaro da za su kare makarantu a Bauchi, ya ƙaddamar da tawagar ne a ranar Alhamis a Bauchi.
A wajen ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na ‘Saɓe Schools’ a ɗakin taro na otal ɗin Hazibal. Ya ce, ta hanyar haɗa kai da masu ruwa da tsaki ne jami’an tsaro za su iya kaiwa ga samar da ingantaccen tsaro a makarantu ga yaran Najeriya.
Egbetokun wanda ya samu wakilcin AIG Abubakar Sadiƙ Aliyu, ya shawarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya yi amfani da ƙwarewarsa da gogewarsa da tunaninsa wajen samar da sabbin dabaru da tsare-tsare masu inganci waɗanda za su inganta tsaro da ƙarƙo a makarantun jihar.
Ya ce, rundunar na daga cikin tsare-tsaren kare lafiya a makarantu da Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun ya ɓullo da shi kuma ya umurci Kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja da su haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaron makarantu daidai da tsarin da aka yi a ƙasa baki ɗaya.
Egbetokun ya bayyana shirin a matsayin wani gagarumin ci gaba ga tsarin da ya haɗa da kare makarantu cikin aminci da sauran muhallin koyo.
Ya ce, ya zama wajibi hukumomin ilimi na Najeriya da shugabannin al’umma su haɗa kai da jami’an tsaro wajen ƙarfafawa da kuma kare makarantun daga duk wata barazana.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, ’yan sanda a shirye suke a kodayaushe don ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da yanayin koyo mai kyau da aminci ga ɗalibai.
Gwamna Bala Mohammed ya ce, ya kamata hukumomin tsaro daban-daban su faɗakar da wasu shugabannin ɗalibai da ƙungiyoyinsu dabarun gano duk wata barazana da sanar da hukumomin tsaro cikin lokaci.
Gwamna Bala wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tsaro, AIG Ahmed Abdulrahman ya shawarci shugabannin ɗaliban da su yi amfani da hanyar da ta dace wajen sanar da Jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani mutum ko wani lamari da ya taso.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omoloro Aliyu ya yi ƙarin haske kan yadda ake samun ƙaruwar satar mutane, hare-hare da tashe-tashen hankula da ake kai wa makarantu, ɗalibai da ma’aikatu.
“Wadannan munanan al’amura ba wai kawai sun kawo cikas ga harkar ilimi ba, har ma sun sanya tsoro da fargaba a tsakanin iyaye, ɗalibai da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya, wanda ’yan sanda tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki daban-daban suka mayar da martani tare da samar da shirin kare makarantunmu cikin aminci.