’Yan sanda sun tayar da kura a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Anambra saboda rashin biyan su kudadensu na aikin zaben.
Fusatattun ’yan sandan sun dauki matakin dagula lissafin tattara sakamkon zaben ne a ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Karamar Hukumar Anaocha ta Jihar Anambra a ranar Asabar da dare.
- ’Yan sanda sun koka kan rashin kudin abinci a zaben Anambra
- ’Yar Sanata Goje ta ajiye mukaminta bayan an kai masa hari a Gombe
Wani mai sa ido kan yadda zaben ke gudana ya ce ana tsaka da aiki ne fusatattun ’yan sandan da aka kai daga Jihar Ondo suka kashe injin janareton da ke samar da wuta a cibiyar tattara sakamakon zaben.
A cewarsa, hakan na iya kawo babbar matsala ga zaben, amma daga baya an samu an shawo kan ’yan sandan, har aka sake kunna janareton aka ci gaba da aiki da shi.
Tun da farko mun kawo muku rahoton yadda wasu ’yan sandan da aka tura domin samar da tsaro a zaben suke kokawa cewa an ki ba su N5,000 da aka ware wa kowannensu a matsayin kudin abinci a lokacin zaben.
Wasu daga cikin ’yan sandan sun bayyana wa wakilinmu cewa yunwa ta yi musu kullin alawa, saboda rashin tanadar musu da kudaden abincinsu.
Kakakin ’yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya tabbatar wa ’yan jarida cewa ’yan sanda kimanin 5,000 ne ba a biya su alawus dinsu da aka ware musu domin aikin zaben ba.
Ya ambato Shugaban ’Yan Dansan Najeriya, Usman Baba Alkali, na cewa wasu kurakurai da aka yi wurin tattara sunayen jami’an da hakan ta shafa ne suka haifar da matsalar.
Mba bayyana cewa shugaban ’yan sandan ya ba da umarnin a sake tura masa sunayen masu matsalar a biya su, domin a cewarsa, sama da mutum 29,000 daga cikin ’yan sanda 34,500 da aka tura aikin sun riga sun samu kudadensu.
A cewarsa, wannan shi ne karon farko da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta biya jami’anta kudaden alawus din aikin zabe kafin ma a fara gudanar da zaben.