Jami’an ’yan sanda a yankin Soba a jihar Kaduna sun mika wa iyalan wani mutum mai suna Mustapha Sanusi da ya yi hatsari ya rasu nan take tsabar kudi Naira miliyan 3,991,650 da aka samu a tare da shi.
Babban Jami’in ’Yan Sanda na yankin, Sufurtanda Pam Daniel Moses ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe goma sha daya na safe a daidai Unguwar Dan Isa kan hanyar Pambeguwa zuwa Zariya.
- An bindige jami’in tsaro a Kaduna
- Za a rufe daukar ma’aikata 774,000 ranar 21 ga Satumba
- ‘Ma’aikatun gwamnati sun yi watanda dan Naira tiriliyan 1.2’
Ya ce garin kauce wa wani rami, Mustapha Sunusi da ke cikin mota Peugeot 206, ya bugi wata mota da ke kan hanyarta ta zuwa Zariya inda wasu fasinjoji suka sami raunuka.
A cewarsa, bayan faruwar hatsarin ne suka samu kira daga wasu mutane da suka sanar da su cewar an yi hatsari kuma akwai mutuwa a daidai Unguwar Dan Isa.
Ko kafin jami’ansa su isa wurin wani dan kishin kasa ya kai wurin inda ya yi nasarar daukar kudin da ke cikin motar mamacin.
A wannan lokaci ne wasu gungun mutane da suka isa wurin suka yi kokarin kwace kudin a hannunsa.
Ana cikin haka ne jami’an ’yan sanda suka isa wurin suka sami nasarar karbar kudin.
Bayan da suka karbi kudin sun kai wadanda suka samu raunuka asibiti don yi musu magani, suka kuma je tare da wasu mutane, inda suka kirga kudin a gabansu aka sami Naira miliyan 3,991,650.
Ya ci gaba da cewa tuni suka mika kudin ga iyalan mamacin ta hannun amimisa Alhaji Kabiru Garkuwan Soba, kuma dukkannin bangarorin biyu wakilansu sun rungumi kaddara sun yafe wa juna, kuma an ba su motocinsu a ranar Talata.
Aminiya ta ji ta bakin iyalan marigayin, inda suka yaba wa mutum na farko tare da jami’an ’yan sanda da suka nuna halin kwarai na mika musu kudin da suka samu a motar dan uwansu tare da motocin da suka yi hatsarin ba tare da sun karbi komai daga gare su ba.
Da Aminiya ta tuntuni Kakakin ’Yan Sanda Jihar Kaduna, ASP Aliyu Jalige ta wayar hannu domin jin ta bakinsa kan lamarin ya ce za kira amma harzu lokacin hada rahoton bai kiraba.