’Yan sandan Jihar Delta sun miƙa Sarkin Ewu, Clement Ikolo Oghenerukevwe ga sojoji bayan rundunar sojin ta ayyana shi a matsayin wanda take nema bisa zargin sa da hannu a kisan sojoji.
A jiya Alhamis ne basaraken ya miƙa kansa ga ofishin ’yan sandan bayan wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar inda a ciki ta bayyana mutum takwas da take nema ruwa a jallo bisa zargin hannunsu a kisan dakarunta 17 a yankin Ughelli na jihar.
Cikin mutanen da take neman har da Farfesa Ekpekpo Arthur, da mahaifiyar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kai harin.
Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar yau Juma’a ne aka miƙa shi ga sojojin, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida mata.
Sai dai basaraken ya musanta zargin da sojojin suke yi masa yayin wani taron manema labarai kafin daga baya ya miƙa kan nasa.
- Tinubu ya halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Delta
- ‘Sojojin da aka kashe sun bar zawarawa masu juna biyu da marayu 21’
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da miƙa Sarkin ga wakilinmu a wani saƙo da ya rubuta.
“Muna da tabbacin Edafe ya amsa saƙon da aka aika masa.
Gabanin miƙa kansa ga jami’an tsaro a birnin Delta, Sarkin ya gudanar da taron manema labarai inda ya bayyana cewa ba shi da laifi.
“Na yi mamakin yadda sunana a matsayin sarkin masarautar zai bayyana a cikin jerin waɗanda ake nema ruwa a jallo.
“Ba ni da hannu a kashe-kashen, ba ni da hannu wajen ƙarfafa wani ya kashe kowa, ya saba wa falsafar da nake kai ɗan Adam da kuma imanina a matsayina na mabiyin Katolika.
“Wannan babban laifi ne ga bil’adama don haka ya kamata su duba wuraren da suka dace sannan su yi cikakken bincike don sanin duk waɗanda suka aikata wannan aika-aika a gurfanar da su a gaban kuliya domin a yi adalci.
“Ni ba hannuna a ciki, kuma kamar yadda na faɗa a baya, gwamnatin jihar tana sane da tashe-tashen hankulan da nake fama da su, kuma a lokacin da nake magana, gwamnati ta yi wani shiri na gayyatar ‘yan adawa kwanan nan kafin faruwar hakan,” in ji shi.
Tuni dai rundunar sojojin ta garzaya da Sarkin Abuja, inda daga can za ta ci gaba da gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
Bayanai sun ce bayan da ‘yan sandan suka mika shi ga Sojoji, an titsiye Sarkin na tsawon sa’o’i kafin a garzaya da shi filin jirgin saman Asaba da wata tawaga karkashin jagorancin kwamandan rundunar soji ta 63 Brigade Asaba, inda aka shilla da shi babban birnin kasar.