✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe ’yan ta’adda da ke neman sace matafiya a Katsina

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bukaci hadin kan jama'a don dakile hari a nan gaba.

’Yan sanda sun kashe wasu ’yan bindiga da suka yi yunkurin tare hanya su sace mutane a hayar Dutsin-Ma zuwa Kankara a Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce ’yan bindigar sun gamu da ajalinsu a hannun jami’an runduanr ne a ranar Lahadi.

Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) sun yi nasarar dakile harin ne bayan samun rahoton ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun tare babbar hanyar Dutsin-Ma zuwa Kankara suna kokarin yin garkuwa da mutane.

“Bayan samun rahoton kwamandan yankin Dutsin-Ma, nan take ya hada tawagar hadin gwiwa na ’yan sanda da ’yan banga suka kai dauki.

“Da isaru wurin, wadanda ake zargin suka bude musu wuta, inda jami’an suka yi nasarar kashe wasu uku daga cikinsu.

“Sai dai wani Masa’udu Sani wanda dan banga ne, ya samu rauni a hannunsa,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Aliyu ya kara da cewa a halin yanzu dan bangar na karbar magani yayin da ake ci gaba da kokarin kamo sauran wadanda suka gudu.

A cewarsa, kwamishinan ’yan sanda a jihar, Aliyu Abubakar Musa ya yaba wa jami’an hadin gwiwar bisa jarumtaka da suka nuna.

Ya bayyana cewa kwamishinan ya kuma bukaci jami’an da su ci gaba da gudanar da aikinsu don tabbatar da tsaro a jihar.

Musa ya roki al’ummar Jihar da su bai wa jami’an tsaro bayanai a kan lokaci kan ayyukan bata-gari, “Domin daukar matakin gaggawa da dakile su.”