✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bar bashin tiriliyan 1.5 a ma’aikatar ayyuka —Umahi

Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bar bashin Naira tiriliyan 1.5 a ma'aikatar

Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar bashin Naira tiriliyan 1.5 a ma’aikatar.

Umahi ya ce ma’aikatar ta kafa kwamitoci shida saboda yankunan siyasa shida na kasar nan domin tantance basukan da ‘yan kwangila ke bin ta.

Ya ce, kwamitocin za su tantance takardun shaidar bashin da gwamnati ta ba wa ’ya kwangilar zuwa ranar da Buhari ya sauka daga mulki.

Za kuma su tantance takardun shaidar bashin da suke bin ma’aikatar daga hawan Shugaba Tinubu zuwa yanzu.

Umahi ya ce tantance basukan da kuma sauyin farashi da aka samu na da muhimmanci, lura da hauhawan farashin kaya.

Don haka ya shawarci ’yan kwangilar da su zo gaban kwamitin domin tantancewa a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.

Sakataren yada labaran ma’aiaktar, Orji Uchenna Orji ya ce, za ya yi tantancewar ne daga ranar Talata 12 zuwa Juma’a 22 ga watan nan na Disamba daga karfe 9 na safe zuwa 7 na dare.