✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga suna shirin kai hari a Kaduna

An kwace bindigogi takwas da harsasai kusan 1,700 a hannun ’yan ta'addar.

Jami’an tsaro sun aika wasu ’yan bindiga lahira a yayin da suke shirin kai hari a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

Kakakin ’yan sandan Jihar, Mohammed Jalige ya ce, makaman da aka kwace a hannun maharan sun hada da bindigogi biyar kirar AK-47 da wasu uku kirar G-3 da harsasai kusan 1,700 da mota kirar Golf 3.

Ya ce, “Bayan samun bayanan sirri cewa ’yan bindigar na shirin kai hari, hadin gwiwar jami’an tsaro sun ritsa ’yan bindigar ne a garin Saminaka.

“Da jin alamun jami’an tsaro sai suka fara harbi, nan take ’yan sanda suka mayar da martani suka bindige biyu daga cikinsu, sauran kuma da aka harba suka jefar da makamansu suka tsere zuwa cikin daji.”

Ya ce an kai gawarwakin ’yan bindigar Asibitin Kwararru na Barau Dikko da ke garin Kaduna, ana kuma ci gaba da bincike don damko sauran.

“Muna rokon jama’a su taimaka da rahoton duk wanda aka gani da raunin harbi, da kuma bayanan da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a fadin jihar,” inji shi.